Connect with us

Manta Sabo

Na janye kalaman ɓata wa A-A Zaura suna a Kotu – Likita

Published

on

Kotun majistrert mai lamba 51 karkashin mai Shari’a Ibrahim Mansur Yola, ta sanya ranar 25 ga wannan watan domin bayyana matsayarta a kan tuhumar da ƴan sanda ke yiwa Dakta Sulaiman Musa Ɗan Takarda da laifin ɓata suna.

Tun da fari dai ƙunshin zargin da a ke yi wa Dakta Sulaiman Musa ya bayyana cewar, a ranar 22 ga watan 2 na wannan shekara Sulaiman ya ɓata wa Abdulkarim Abdussalam, A-A Zaura suna, ta hanyar yaɗa wasu maganganu a shafinsa na Facebook, inda ya kira shi da Ɗan Damfara.

A zaman kotun na yau mai kara A-A Zaura ta bakin wakilinsa Alhaji Ado Zaura, sun bayyana cewar sun janye ƙarar da suke akan wannan matashi.

Wakilinmu na Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa yayin zaman kotun, matashin ya janye kalamansa har ma ya ce sharrin shaiɗan ne kuma ba zai sake ɓata sunan wani ba.

Manta Sabo

Iyalan Marigayi Sharu Ilu sun sake samun nasara akan Aminu Ɗantata a Kotu

Published

on

Kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako, ta sake tabbatar da hukuncin kotun kasa na mallakawa iyalan marigayi Sharu Ilu wani rami da ke unguwar Gwammaja, da suke shari’a da Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata sama da shekaru huɗu.

Kotun ɗaukaka ƙarar da ke nan Kano mai alƙalai uku, wanda mai shari’a, Justice Ugo ya jagoranci zaman, ta sake tabbatar da hukuncin kotun kasa bayan da ɓangaren Alhaji Aminu Ɗantata suka nemi kotun ta basu izinin tafiya kotun koli domin sake ɗaukaka ƙara.

Akan roƙon da suka ɗin dai kotun ta ce sun makara bisa yadda tuni wa’adin ɗaukaka ƙarar ya ƙare, kamar yadda tashar Dala FM Kano, ta rawaito.

Continue Reading

Manta Sabo

Zaɓen ƙananan hukumomi: Kotu ta dakatar da hukumar Zaɓe ta Kano daga karɓar kuɗin Form ɗin da ta saka.

Published

on

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano Kanseic, daga karɓar Naira milyan goma a matsayin kuɗin sayar da Form ɗin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, da kuma Naira miliyan biyar a matsayin na Kansiloli a jihar nan.

Wannan ya biyo bayan yadda jamiyyun APP da ADP, da kuma SDP na jihar Kano, suka shigar da hukumar kara a gaban babbar kotun tarayyar, suna kararta da ta dakatar da karɓar kudin har sai an kammala jin karar.

Da yake yiwa Dala FM Kano ƙarin bayani kan ƙarar, sakataren jam’iyyar ADP, mai kula da jamiyyar a arewacin kasar nan Tijjani Lawan Kofar Wambai, ya ce sun shigar da ƙarar ne bisa yadda kuɗaɗen da hukumar ta saka suka yi yawa, kasancewar karbar kudin ka iya bude hanyar cin hanci da rashawa.

A ranar 15 ga watan Agustan 2024, ne dai hukumar zaɓen ta jihar Kano, ta sanya Naira miliyan goma a matsayin kuɗin sayan Form na tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, yayin da ta ce za’a biya Naira miliyan biyar a matsayin na Kansiloli, inda za’a gudanar da zaɓen a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.

Continue Reading

Manta Sabo

Wasu ƴan mata sun tayar da bori a kotu bayan an tsalala musu Bulala

Published

on

Kotun majistret mai lamba 51 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, ta hori wasu ƴan mata da ɗaurin watanni 6, ko kuma zabin tarar dubu tamanin-tamanin kowanne su, da kuma karin bulala shida-shida haɗi da sharar banɗaki ta sati uku.

Tunda fari Ƴan Sanda ne suka gurfanar da ƴan matan bisa zargin su da yawan banza, da tayar da hankalin al’umma, da kuma laifin Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Yayin da aka karantawa ƴan matan ƙunshin tuhumar da ake yi musu sun amsa laifin nasu har guda goma sha Shida.

A yayin zaman kotun ta tambaye su dalilin da ya sanya suke yawon banza, inda suka bayyana mata cewar suna fitowa ne daga gaban iyayensu idan sun kammala yawace-yawacen sai su koma gida.

Mai Shari’a Hajara Safiyo ta kuma umarci ƴan matan da su zama mutanen kirki idan sun gama zaman gidan gyaran halin.

Wakilin Dala FM Kano Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, jim kaɗan bayan kammala hukuncin sai ƴan matan suka fara koke-koke hadda hawa bori a kotun, bisa shiga furgicin da suka yi kan hukuncin.

Continue Reading

Trending