Connect with us

Manyan Labarai

Muna gargaɗar gwamnoni kan hana Zanga-zangar lumana a Najeriya – War Against Injustice

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam, da yaƙi da rashin adalci, da bibiya akan shugabanci na gari, ta War Against Injustice, ta gargaɗi gwamnoni a Najeriya, da su gujewa hana mutanen jihohin su yin zanga-zangar lumana a kan kuncin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan ƙungiyar ta War Against Injustice, Kwamared Umar Ibrahim Umar, ne ya fitar mai ɗauke da sa hannun sa, aka rabata ga manema labarai a Talata a Kano.

Sanarwar ta ƙara da cewa ba dai-dai ba ne gwamnonin su hana ƴan kasa cin gajiyar haƙƙin da kundin tsarin mulkin kasa, da sauran dokokin Duniya wanda Najeriya ta saka hannu da kuma tsarin mulkin Dimokaradiyyar ya basu, kan fitowa su nuna kunci da tsadar rayuwar da suke ciki.

Kwamared Umar Ibrahim ya kuma ja hankalin jami’an tsaro da kada su sake su tilasta duk wani umarni da gwamnonin za su bayar dangane da hana zanga-zangar lumanar a jihohinsu, domin doka tayi tanadin duk umarnin da gwamnonin zasu bayar, indai ya saɓawa doka to kada jami’an tsaro su tilasta binsa.

Ya ci gaba da cewa, “Ƴan Najeriya ku yi zanga-zangar da za’a gudanar cikin lumana tare da girmama dokokin kasa da kuma haƙƙoƙin Jama’a, “in ji shi”.

Idan ba’a manta ba, ƙungiyar ta sanar da shirinta na jagorantar zanga-zangar lumana a birnin Kano, domin yin kira ga gwamnati da ta yi duba akan halin matsin da al’umma suke ciki wanda ya janyo a hankali mutane su na mutuwa a halin yanzu.

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta ɗage komawar ɗalibai makarantu Firamare da na Sakandire

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ɗage komawa makarantun Firamare da na Sakandire daga ranar Lahadi da Litinin, har zuwa wani lokaci da za a saka a nan gaba.

Kwamishinan Ilmi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Asabar 07 ga watan Satumban 2024.

Doguwa ya kuma ce gwamnatin ta yi niyyar buɗe makarantun kwana ne daga gobe Lahadi, yayin da na jeka ka dawo kuma ana kuɗiri aniyar buɗewa daga ranar Litinin, amma sakamakon wani abu na gaggawa da ya taso ya sanya aka ɗage komawa makarantun zuwa wani lokaci da za’a saka a nan gaba.

Kwamishinan Ilmin ya kuma bai wa iyayen yara haƙuri bisa jinkirin komawa makarantar da aka samu, wanda ya ce an yi hakan ne domin cikar daraja da mutumtakar ƴaƴan su, da kuma ƙara shiri akai.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun cafke yaron da suke satar Adai-dai ta sahu da wasu matasa a Kano – Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snaching

Published

on

Rundunar tsaro da ke yaƙi da ƙwacen waya da faɗan Daba da kawar da Shaye-shaye ta Anti-Phone Snaching da ke jihar Kano, ta samu nasarar cafke wani Yaro da bai wuce shekaru 14 ba, da ake zargin wasu matasa sun haɗa kai da shi suka saci wani baburin Adai-dai ta sahu a unguwar Gammaja Tagwayen Gida.

Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snaching, Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyanawa Dala FM Kano a ranar Juma’a, ya ce sun cafke matashin da baburin ne a cikin tsakar daren Laraba da misalin ƙarfe 04:00, a lokacin da suke sintiri, inda suka ci karo da matasan.

“A lokacin da muka yi kan matasan su huɗu da suke cikin baburin Adai-dai ta sahun inda uku suka tsere muka samu nasarar cafke Yaron ɗan unguwar Ɗorayi da Babur ɗin, amma muna ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin kamo sauran matasan, “in ji Inuwa Sharaɗa”.

Kwamandan rundunar ya kuma ce a lokacin da suka cafke yaron ana tsaka da ruwan sama ne har ma ruwan ya jiƙa su sosai bisa rashin rigar ruwa da suke fama dashi, tare da fuskantar ƙarancin kayan aiki, har ma guda cikin ma’aikatan su ya faɗi tare da jin ciwo.

Hamisu Ahmad, shine Ma-mallakin Babur ɗin, ya ce a lokacin da aka sace masa baburin ya matuƙar shiga cikin damuwa duk da dai satar Babur ɗin shine karo na biyu.

Yaron da rundunar ta kama ya shaidawa Dala FM Kano cewa, su huɗu ne suke fita satar baburin Adai-dai Sahun, da kuma satar wayoyin mutane idan an ɗauka su sayar, amma ya yi nadama idan aka sake shi zai koma makaranta duk da mahaifin sa ya kareshi daga gidan su.

A cewar sa, “Mahaifina ya koreni nida ƙanena saboda yadda muke ƙin zuwa makaranta, amma dai idan na fita zan koma in bashi haƙuri domin nima abin ya dameni, “in ji yaron”.

Mai baburin ya kuma miƙa godiyar sa ga Allah S.W.T. tare da godewa jami’an rundunar bisa nasarar da aka na ganin Babur ɗin nasa har ma aka kama yaron da ake zargin sun sace ɗan sahun.

Majiyar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, Inuwa Salisu Sharaɗa ya ƙara da cewa za su zurfafa bincike akan al’amarin gabanin bai wa wanda ya zo ya ce babur ɗin nasa ne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ruguzowar Gini ya yi sanadiyyar rasuwar mutane uku da jikkatar wasu a Kano

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane uku a unguwar Sabon gari yankin Noman’sland da ke ƙaramar hukumar Fagge a Kano, sakamakon yadda gidan da suke mai hawa biyu ya ruguzo musu su biyar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar PFS Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyanawa Dala FM Kano, hakan a ranar Alhamis, ya ce iftila’in ruguzowar ginin ya rutsa da mutane biyar biyo bayan mamakon ruwan saman da akayi a daren jiya Laraba.

Ya ce bayan da aka kai su Asibiti ne likitoci suka tabbatar da rasuwar mutane uku yayin da biyu suke karɓar kulawar likitoci.

Saminu Yusif ya kuma tabbatar da ruguzowar wani gini mai hawa ɗaya a unguwar Sharaɗa Turba layin Service da ke ƙaramar hukumar Birni, da ya faɗawa mutanen gidan su shida, inda jami’ansu suka kai su Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, yayin da suke karɓar kulawar likitoci.

A cewar sa, “Mun kuma samu labarin yadda wani gini mai hawa ɗaya da gaban gidan ta ruftawa mutane uku a unguwar Ƙofar Nassarawa Movie Quarters, daga bisani jami’an mu suka kai ɗauki, “in ji Samun Yusif”.

SC Musbahu ya ƙara da cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa ne akan iftila’in ruftawar gine-ginen a ranar Alhamis, daga ɓangarorin da al’amarin ya faru, inda jami’ansu suka kai ɗaukin gaggawa.

Continue Reading

Trending