Labarai
Ya kamata a gaggauta isar da tallafin da aka samu ga iyalan waɗanda iftila’in tankar Mai ya rutsa da su a Jigawa – Human Right

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa, da ta gaggauta isar da tallafin da gwamnatoci da kuma wasu manyan mutane suka bayar ga waɗanda iftila’in fashewar tankar dakon man fetur ya rutsa da su a garin Majia da ke ƙaramar hukumar Jigawa, al’amarin da ya shafi sama da mutane 250.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar na ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan yayin zanatawar sa da tashar Dala FM Kano, a ranar Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai wata babbar motar dakon man ta samu haɗari a garin Majia da ke jihar ta Jigawa, inda ta kama da wuta da hakan ya yi sanadiyyar rasuwar kusan mutane 170, yayin da fiye da mutum 100, ke kwance a Asibitoci daban-daban da suke karɓar kulawar likitoci bisa ƙonewar da sassan jikin su ya yi.
Tasi’u Idris ya kuma jajanta wa gwamnati da dukkanin al’ummar jihar Jigawa, kan faruwar al’amarin inda ya kuma miƙa ta’aziyyar su da jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa dasu.
A cewar sa, “Muna kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta gaggauta gyara wurin da motar dakon man ta yi haɗari bisa yadda titin yake haddasa haɗari tare da asarar rayuka da kuma dukiyoyin al’umma a wurin domin daƙile faruwar irin hakan a gaba, “in ji Soja”.
Rahotanni sun bayyana cewar yanzu gwamnoni da manyan ƴan kasuwa da ƴan siyasa da dama ne suka bayar da gudunmawar su domin ragewa iyalan waɗanda lamarin ya shafa wani raɗaɗi, inda zuwa yanzu aka samu sama da tallafin Naira Miliyan dubu ɗaya.

Addini
Hajji2025: Maniyyatan Najeriya 16,182, sun sauka a Saudiyya – NAHCON

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce izuwa yanzu aƙalla maniyyatan ƙasar su 16,182, ne suka sauka a ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2025.
Hukumar ta NAHCON, ta bayyana hakan ne da yammacin Alhamis ɗin nan a shafinta na Facebook, ta ce aƙalla jirage 40, ne suka yi jigilar maniyyatan, daga ranar juma’ar da ta gabata, da aka fara kai maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.
NAHCON, ta ƙara da cewa, jirgi na ƙarshe da ya sauka a Madinah, shi ne jirgin UMZA, mai lamba UMZ3412, da ya tashi ɗauke da maniyyatan jihar Kaduna su 299, Maza 229, mata kuma 70, sai wasu na musamman su 9.

Labarai
Rashin taimaka wa masu buƙata ta musamman ya sa suke barace-barace – Sarkin Dawakin Makafin Kano

Sarkin Dawakin Makafin Kano Abubakar Ibrahim Gwarzo, ya ce samar wa masu buƙata ta musamman guraben aiki ka iya taimaka musu wajen ficewar su daga yawaitar barace-barace a tsakanin al’umma.
Abubakar Ibrahim Gwarzo, na wannan jawabin ne a yayin da gidauniyar tallafawa masu buƙata ta musamman da mabuƙata ta Marigayi Farfesa Jibril Isah Ɗiso, ta bai wa masu lalurar gani su 25, tallafin Kuɗi aƙalla Naira dubu goma goma, da dubu ashirin-ashirin ga kowannen su, a Firamaren Dala da ke unguwar Makafin Dala, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.
“Duba da yadda masu bukata ta musamman suke da kaifin basira, akwai buƙatar a rinƙa samar musu guraben ayyukan yi domin su dogara da kan su, “in ji Gwarzo”.
Abubakar Ibrahim, ya kuma shaidawa Dala FM Kano, cewa, masu buƙata ta musamman suna cikin wani hali mawuyacin hali, musamman ma da rashin taimaka musu yake sanya ake samun wasu na yin barace-barace a tsakanin al’umma.
“Masu lalurar gani suna iya ƙirga abubuwa, kamar irin su Sabulu, da yin sauran abubuwa, idan aka dauke su aiki hakan zai taimaka musu tare da kaucewa faɗawar su a cikin barace-barace, “in ji shi”.
Gwarzo, ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya tuna da alkawarin da ya yi musu a lokacin yaƙin neman zaɓen sa, kan taimaka wa masu buƙata ta musamman idan ya samu nasara, lamarin da ya ce zuwa yanzu ya ci tura, a don haka suke kira ga gwamnan da ya kai musu ɗauki.

Labarai
Gwamnatin Kano ta biya sama da Biliyan uku don biyawa ɗalibai kuɗin jarabawar Qualifying a jihar

Gwamnatin Kano ta amince da kashe aƙalla sama da Naira Biliyan dubu ɗaya, don biya wa ɗaliban jihar kuɗin jarabawar neman shiga makarantun gaba da Sakandire ta NECO, domin sauƙaƙa musu a fagen karatunsu.
Kwamishinan Ilmi na jihar Kano Dakta Gwani Haruna Makoɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Juma’a, ya ce ɗalibai 141,715, ne suka rubuta jarabawar neman cancantar ta samun damar rubuta jarabawar NECO, kyauta, daga gwamnatin, ko kuma ɗalibi ya biya da kan sa kuɗin jarabawar da akafi sani da Qualifying.
A cewar sa, “Ɗaliban da suka samu nasarar gami da cancanta da za a biyawa kuɗin daga gwamnatin Kano, sun samu sakamako biyar zuwa sama ne ga kowanne su, kuma kaso saba’in da biyar cikin ɗari na ɗaliban sun samu nasara, “in ji Gwani Makoɗa”.
Kazalika, Makoɗa, ya kuma ce wannan na daga cikin ƙudirin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin haɓaka ilmi da ƙara haɓaka tattalin arziki, da kuma tallafawa karatun Ɗalibai musamman ma Matasa, da taimaka wa Iyaye a faɗin jihar, lamarin da ya ce Abba ya cika Gwarzo wajen kula da ilmi da sauran ɓangarori a Kano.
Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa, Kwamishinan na ilmi a Kano Gwani Ali Haruna Makoɗa, ya kuma buƙaci shugabannin makarantun gwamanti a jihar, da su tabbatar da cewar kowanne ɗalibi ya cancanci sanin sakamakon sa ba tare da wani sharaɗi ba.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su