Connect with us

Labarai

HUKUMAR HANA FASA KAURI TA KASA  TA KAMA KAYAYYAKIN SAMA DA NAIRA MILIYAN CASA’IN.

Published

on

Hukumar hana fasa kauri ta kasa mai kula da jihohin Oyo da Osun ta kama buhunhunan shinkafa da tsofaffin tayoyi da dilolin gwanjo da man girki da aka kiyasta kudinsu ya dara Nera miliyan casa’in.

Alhaji Tanko Bayero Muhammad mataimakin kwanturolan kwastan dake kula da shiyyar yace, “Sun kama manyan motocin ne a karamar hukumar Iwajowa cikin jihar Oyo.

Ya kara da cewa, kamar yadda hukumar kwastan take da masu bata bayanan sirri, su ma yan Simoga suna da masu basu bayanan sirri, saboda haka kayan kawai suka samu damar kamawa tare da direba daya, yayin da sauran suka tsere.

Labarai

Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.

“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.

Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Continue Reading

Labarai

Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Published

on

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.

Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.

Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.

Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

Continue Reading

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Trending