Connect with us

Labarai

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA FARA FITAR DA ZOBO KASAR WAJE.

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, “Ta shirye tsaf domin fara safarar zoborodon da al’ummar jihar suke  nomawa zuwa kasar Mexico”.

Gwamnan jihar ta Jigawa wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Barista Ibrahim Hassan Hadeja ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai jiya Laraba a ofishinsa.

Ya ce,” Wannan yunkuri ya biyo bayan amincewar da wasu masana suka yi kan cewa Zoborodo da manoman Jigawa ke nomawa na sahun gaba cikin  ingantaccen zobo da ake bukata”.

Mataimakin gwamnan ya kara da cewa,” Tuni dai wasu kasashe ciki harda kasar Mexico suka nuna sha’awarsu na siyan wannan zobo yadda suka amince da tallafawa manoman da ingantaccen iri da taki domin bunkasa noman na Zobo a fadin jihar”.

Haka kuma ya yi kira da manoman jihar dasu garzaya domin yin rijista tareda gujewa yin algus domin cin moriyarsu da bunkasa tattalin arzikin jihar baki daya.

Labarai

Masu koyarwa a aji su ci gaba da zama a gida – KSSSMB

Published

on

(more…)

Continue Reading

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish