Connect with us

Labarai

Lodi fiye da kima – Dalibi ya rasa ransa a kano

Published

on

Wani dalibin Makarantar Arabiya ta S.A.S ya rasu yayin wani hatsari da yayi sanadiyar jikkatar wasu dalibai da dama a Unguwar Dan Agundi dake nan Kano.

Hadarin ya afku ne da tsakar Ranar jiya Talata a wurin juyawa dake kusa da ofishin hukumar kula da gyaran tituna ta jaha wato KARMA, lokacin da mai baburin da ya dauko daliban su fiye da bakwai ya tuntsire a tsakiyar titi daidai lokacin da wani mai mota ke tsaka da tsala gudu yayi karo da adaidaita sahun da daliban suka fadi, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaidawa wakilin mu Abba Isah Muhammad

 

Mun kuma tuntubi Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kano Saidu Muhd Ibrahim,ta wayar hannu game da lamarin.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa lokacin da ya ziyarci sashin bada agajin gaggawa na asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da yammacin jiya ya tarar ana kokarin fita da gawar dalibin da ya rasu yayin da likitoci ke kokarin ceto rayuwar sauran daliban da suka karye da wanda suka jikkata.

Rahotanni dai sun bayyana cewar a baya Gwamnati ta dauki matakin rufe gurin juyawar dake kusa da makabartar ta Dan Agundi sakamakon yawan samun hatsari daga baya kuma ake zargin wani da tilasta bude gurin.

Al’umma dai na jira don ganin matakin da gwamnati zata dauka don kare rayuka da dukiyoyin Jama’a.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending