Connect with us

Siyasa

Nanono kaji tsoron Allah ka fadawa Buhari gaskiya –Aminu Gurgu mai fulo

Published

on

Nanono kaji tsoron Allah ka fadawa Buhari gaskiya –Audu Gurgu mai fulo

Cikin wata tattaunawa da shirin Hangen Dala yayi da Alhaji Aminu Gurgu Mai Fulu na jam’iyyar PRP ya bukaci ministan Noma Alhaji Sabo Nanono da yaji tsoron Allah ya fadawa shugaba Buhari halin da talakan Nigeria ke ciki.

Mai fulo ya roki minstan da yayi koyi da ministan wutar lantarki da ya fito ya fadawa al’ummar Nigeria gaskiya game da aikin wutar lantarki a mambila.

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu na mai fulo?

Nanono kaji tsoron Allah ka fadawa Buhari gaskiya –Audu Gurgu mai fulo

RUBUTU MAI ALAKA:

Bana sakawa dalibai na mari –Mallam Mamman mai ‘yan mari

Dambarwa ta barke tsakanin masu lodin ababan hawa da KAROTA

Kotu ta bada belin sadiya Haruna

Continue Reading

Labarai

Majalisa ta fara tantance kwamishinoni

Published

on

Da safiyar yau Talata ne majalisar dokokin jihar kano ta fara tantance sabbin kwamishinonin da gwamna Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya aike da  sunayen wanda yake son ya nada a matsayin kwamishinoni don neman sahalewar su.

Wakiliyar mu Khadija Ishaq Muhammad ta rawaito cewa tunda misalin karfe 9 na safiya, wasu daga cikin mutanan da majalisar za ta tantance suka fara halarta zauren majalisar don tantancesu.

Rahotanni daga zauren majalisar na bayyana cewa majalisar ta gayyaci tsohon kwamishinan yada labarai kwamared Muhammad Garba domin yin dan takaitaccen jawabi, sai kuma Musa Iliyasu Kwankwaso.

Tuni dai tantancewar tayi nisa ga kunshin kwamishinonin da gwamnatin jihar ta mika sunayensu a jiya litinin, wanda kuma ake sa ran za’a rantsar dasu da zarar majalisar ta kammala aikin tantancewar

Continue Reading

Siyasa

Gwamnati bata bincikar masu uwa a gindin murhu -Kwamaret Bello Basi

Published

on

Matashi dan gwagwarmaya Kwamaret Bello Basi Fagge ya bayyana cewa akwai bukatar a rika karbe kadarorin shuwagabannin da ake zargi da rashawa tun a lokacin da ludayinsu ke kan dawo, mai makon sai sun sauka daga mukamansu.

Ta cikin shirin Hangen Dala na nan Dala FM Kwamaret Basi ya kara da cewa akwai bukatar mahukunta su rika bincikar daukacin manyan jami’an da ake zargi ba sai iya wadanda suke cikin jam’iyyar adawa ba.

“A yanzu fa ta bayyana karara cewa matukar karanka ya kai tsaiko a wannan gwamnatin, matukar kana da uwa a gindin murhu, duk irin laifin da ka tafka babu abinda za’a yi maka, ga mutane da dama wadanda ake zargi amma saboda ‘yan fada ne ba zama a bincikesu ba”

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Munyi hannun riga da rashawa- Hisba

Mun kawo karshen garkuwa da mutane.

An bude gidan abincin naira 30 a kano

Continue Reading

Labarai

An dage cigaba da sauraron karar shugaban KAROTA

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 8 karkashin mai shari’a justice Usman Na’abba ta sanya ranar 14 ga watan gobe domin sauraran martani daga bakin wani lauya mai suna M.S Waziri a cikin kunshin wata kara wadda barrister Rabi’u Sa’idu Rijiyar lemo ya shigar.

Yana karar gwamnatin kano da shugaban hukumar karota Baffa Babba Dan agundi.

Mai karar ta bakin lauyansa barrister Abubakar Sadik Usman ya roki kotun da ta tunbuke Baffa Babba Dan agundi daga shugabancin hukumar.

Masu karar sun bayyanawa kotun cewar sashi na 11 sakin layi na 2 na dokar da ta kafa karota a shekarar 2012 ya zaiyano mutanen da suka cancanta su shugabanci hukumar kuma Baffan baya cikin wadanda suka cancanta.

Lauyan da yake Kare Baffa Barrister M.S. Waziri ya bayyana wa kotun cewar zai shigar da takardun suka akan ko kotun tana da hurumin jin karar, ko masu karar suna da hurumin shigar da karar.

Shima lauyan gwamnati Abubakar Sadik ya bayyana cewar zai shigar da takardun suka.

An kuma sanya 14 ga watan gobe dan jin martanin

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish