Connect with us

Baba Suda

Wasu iyaye mata sun gudanar da zanga-zanga

Published

on

Wasu iyaye mata sun gudanar da wata zanga-zangar lumana Sabo da zargin cewa wani attajiri ya gine  musu hanyar zuwa gidajensu da wani Alhaji Yusuf ya basu tun sama da shekaru 35 a Unguwar Farawa.

Matan wadanda mafi yawansu mazajensu sun rasu ,sun barsu da marayun ‘ya’ya, sunce asalin hanyar wadda gidaje sama da dari suke amfana da ita, wani bawan Allah Alhaji Yusuf ne ya mallakawa al’ummar yankin ita.

Ta hannun babban limamin garin malam Muhammadu Sani Jibril, Inda bayan rasuwar wanda ya bayar da hanyar, sai wannan attajiri mai suna  Alhaji Inuwa ya gine hanyar tare da hadeta cikin wani katon filinsa da yake tsaka da ginawa yanzu.

A zantawar da gidan radiyon Dala yayi da limamin unguwar jim kadan  bayan kammala zanga-zangar, ya ce da farko wakilin attajirin  ya shaida musu cewa za’a bar musu hanyar amma kuma sai suka ga an gineta.

Har ila yau, mun tuntubi wakilin attajirin mai suna Mika’il amma sai ya ce ba zai magana ba har sai ya nemi izinin mai wajen.

Rahotanni na nuni da cewa shi wannan mutumi fitacce ne kuma sanannen mai kudi ne a jihar Kano.

Baba Suda

Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya

Published

on

Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.

An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.

Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.

Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.

Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Continue Reading

Baba Suda

Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli

Published

on

Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.

Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.

Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.

Continue Reading

Baba Suda

Rahoto: Zan bayar da kudin fansa domin a dawo da Kyanwa ta – Matashi

Published

on

Wani matashi a yankin unguwar Farawa dake karamar hukumar Kumbotso, Kawu Rufa’I, ya ce a kan Magen da ya ke zargin an yi masa garkuwa da an raba shi da abar kaunar shi, sakamakon yadda suka shaku da juna.

Kawu Rufa’I yacce zai dauki matakin shari’a mudum ya yi artabu da mutum da ya yi garkuwa da Magen, wanda ya bayyana cewa tun a baya sai da a ka dauke ta duk da furucin da a ka yi masa cewa za a dauke ta.

Wakilin mu Tijjani Adamu wanda ya tattauna da matashin ya aiko mana rahoto.

Continue Reading

Trending