Connect with us

Baba Suda

‘Yansanda sun chafke matar da ake zargi da satar yara

Published

on

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta sake kama wata mata da ake zargin ta dauki wani almajiri za ta tafi dashi, bayan kuma an kamata sai ta nuna wani hoto tace danta ne ya bata tun yana karami.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa  yace matar mai suna Sukaila ‘yar kasar Ghana an yi zargin ta kama karamin almajirinne a unguwar Na’ibawa mai kalwa, tana kuma shirin tafiya da shi ne, sai wani mutumi ya ganta ya kuma hanata tafiya da shi.

Amma  sai ta fito da wani hoto ta nuna  ta kuma ce danta ne wanda ya bata tun yana karami.

A zantawar wakilinmu Nasir Khalid Abubakar da wasu shedun gani da ido sunce  kwata-kwata babu wata kama ko wata alama dake  nuna cewa yaron dake jikin hoton shi ne wannan almajirin data dauka.

Daga bisani dai an je makarantar su almajirin aka kira mahaifinsa don ya gaggauta zuwa ya dauki yaron sa.

Yanzu haka dai matar tana wajen ‘yansanda a tsare, su kuma suna fadada bincike a kanta.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Baba Suda

Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya

Published

on

Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.

An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.

Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.

Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.

Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Continue Reading

Baba Suda

Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli

Published

on

Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.

Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.

Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.

Audio Player



Continue Reading

Trending