Connect with us

Manyan Labarai

Yadda zaka shigar da korafi akan yan sanda.

Published

on

A tashin dai zaka iya ganin sa cikin kayan sarki na gaskiya, ma’ana kayan da jami’an yan sanda suke sanyawa yayin da suke bakin aiki.Shaida ta biyu itace katin shaida wato ID card, wanda ya sha banban da sauran katunan hukumomi da aka saba gani. Katin shaida na dan sanda yana dauke da tambarin giwa, sai kuma sunan mai shi da lambar sa, da kuma sa hannun shugaban yan sanda na kasa. Bayan katin kuwa yana dauke ne da bayanan mallaka na rundunar ta kasa, bayanan dake kasancewa iri daya dana jikin kowanne irin katin shaidar da hukumar ke rabawa jamianta.

Yaya zanyi idan jami’in tsaro ya shiga gaban abin hawa na, ko kuma ya kama ni?

Cikin wata tattaunawar mako da muka yi da kakain yan sanda na jihar kano ASP Abdullahi Haruna Kiyawa yau talata, yace hanya da mutum zai bi shine a tashin farko ya nemi sanin wanda ya kama shi, daga wacce tasha ko ofishi na rundunar?Watakila wannan tambaya tazo wa mai jinta da wani sabon al’amari, ko kuma wani yayi tunanin hakan bai yiwuwa ka tambayi hukuma daga inda aka fito.Abdullahi Haruna yace babu wata matsala tunda duk dan sanda, da ya san aikin sa, zai yi faron ciki da jin wannan tambaya daga wanda ya kama, kuma zai bayar da amsa babu bata lokaci.Kakakin yace sanin kowa ne wasu bata gari kan fake da rundunar domin aikata laifukan da zasu bata suna, matukar kuwa al’umma suka nemi sani, to kuwa zasu jefa shakku a zukatan jami’an tsaro na bogi.ASP Abdullahi Haruna yace a yau talata rundunar ta cafke wani dan sanda bogi, wanda yake dauke da katin shaida na hukumar, bayan da ya tare wani mutum domin karbe masa yan kudade. Sai dai bai yi nasara ba tunda wanda aka kama din yayi amfani da nambobin kota kwana, domin neman daukin rundunar, inda nan take suka yi dirar mikiya tare da cafke shi.A cewar sa akwai bukatar al umma suyi amfani da kwarewar neman sanin wajen neman ba’asi daga yan sanda da suka nemi karbar na goro a hannun su, sannan akwai kyutuwar su karbi nambobin waya na ofisoshin yan sanda da jami’an su, musamman wadanda ke kusa dasu domin neman shawarwari da baasi idan suka samu kai a hannun irin wadannan jami’ai.ASP Kiyawa ya bukaci al’umma su ziyarci shafukan sada zumunta na zamani, domin daukar nambobin waya da rundunar ta ajiye domin amfanin al umma. Ko kuma bibiyar ayyukanta kai tsaye a shafukan na twitter, instagram da facebook.Bisa sauye sauye da sabon kwamishinan yan sanda na jihar kano Habu Amadu Sani yazo, kwamishinan ya umarci a dora lambobin baturan yan sandan kananan hukumomi akan manhajar opera, domin amfanin al umma.Haka kuma ya zayyano wasu nambobin hukumar na bangaren kar ta kwana kamar: 08032419754, 08123821575.Haka kuma zaka iya shigar da korafi akan duk wani jami’in dan sanda da ya aikata masa ba dai dai ba akan lambar waya: 09064525249, 08150202029.Haka kuma rundunar tana da akwatun wasiku na gmail akan: kanopolicepubliccomplaintdesk@gmail.comA karshe kakakin na yansandan jihar kano ASP Abdullahi Haruna Kiyawa yace suna karbar korafe korafe da shawarwarin al umma ta cikin wannan shiri domin amfani dasu a zahirance.

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending