Connect with us

Manyan Labarai

Hukumar Hisba ta tarwatsa gidan wata kawaliya.

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi nasarar tarwatsa gidan wata mata da ake zargin ta na kawalcin maza da mata a unguwar Danbare, inda aka yi zargin wasu ‘yan matan na tarewa a gidan suna aikata Badala.

Daga cikin wadanda ake zargin sun tare a gidan har da wata matashiya Hadiza wacce ta bar gidan iyayenta su ke ta neman ta.

Daga bisani dai iyayen nata su ka je hukumar ta Hisba domin ta nemo ma ta ‘yar ta su, inda hukumar ta baza jami’anta suna bin gidajen da ake zarginsu da aikata badala, bincikensu kuma ya gano cewar ta na gidan matar da ake zarginta da yin kawalci, su ka kamo ta da sauran wasu matan har dama ita matar da ake zargin, kuma da zuwan su hukumar aka fara yi musu gwajin cutar HIV.

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya zanta da wani daga cikin ‘yan’uwan samarin da aka kama a gidan inda ya ce, “Wannan ita ce take jan su, saboda kamar yadda aka fada wannan tsohuwa kowa ya na ganinta za ta je ta samu yaran (may be) kila cikin iya magana, kuma wannan yaro sana’arsa ma kafinta ya na taimakawa iyayensa, musamman ma mahaifiyarsa, idan aka je aka gaya ma ta za ta ce ba halinsa ba ne.

Matasan da aka kama a gidan sun nuna nadamar su, kuma su ka ce wannan shi ne karo na karshe ba za su kuma aikatawa ba.

Sai dai wacce ake zargin, ta ce ba za ta yi magana a rediyo ba, inda ta kuma bada hanzarinta da cewar, ita ba kawaliya ba ce kasuwanci ta ke a wannan gida.

Mataimakin Babban Kwamandan hisbar kan al’amuran yau da kullum wanda Malam Tasi’u Ishak ya ce, “Babu shakka duk inda kaga tsohon banza to asali yaron banza ne, saboda haka idan aka samu irin wannan, matakin da za’a dauka shi ne mataki na hukuma, ta yadda za a kai ga alkali, shi kuma alkali ya yi hukuncin da ya dace.”

Ya kuma kara da cewar, “Duk sanda namiji ko mace ya dauki harkar fasikanci sana’a, to ya na kan fadawa cikin garari, saboda haka tabbacin akwai cutar ko babu sai (result) sakamako ya fito, daga nan ne mutum zai san babu, kuma ko mutum yaga babu bai hana anjima ya kamu da cutar ba idan ya ci gaba da yi.”

Wakilin namu ya so jin ta bakin ‘yan matan suma amma sai su ka ki cewa komai.

Manyan Labarai

Limami: Kar mu yadda a tunzura mu tare da kashe kan mu da dukiya

Published

on

Limamin masallacin marigayi Umar Sa’id Tudunwada da ke harabar gidan rediyon Tukuntawa, Dr Abdullahi Jibril Ahmad ya ce, matasa kada mu yarda a zuga mu har mu lalata dukiyar mu ko kashe kawunan mu.

Dr Abdullahi Jibril Ahmad, ya bayyana hakan yayin da yak e yiwa wakilin mu Tijjani Adamu karin haske a kan abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Babu zanga-zanga a musulunci domin neman wata bukata – Liman

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Bompai SP Abdulkadir Haruna ya ce, rayuwar al’umma ba za ta inganta ba matukar babu zaman lafiya.

SP Abdulkadir Haruna, ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad jim kadan bayan idar da sallar juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yada karya a kafafen sada zumunta – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya ce, al’umma su guji yada karya a kafafen sadarwa na Internet wanda hakan kan janyo fitina a cikin al’umma.

Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya bayyana hakan a hudubar sa da ya gudanar a masallacin na Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!