Connect with us

Manyan Labarai

Hukumar Hisba ta tarwatsa gidan wata kawaliya.

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi nasarar tarwatsa gidan wata mata da ake zargin ta na kawalcin maza da mata a unguwar Danbare, inda aka yi zargin wasu ‘yan matan na tarewa a gidan suna aikata Badala.

Daga cikin wadanda ake zargin sun tare a gidan har da wata matashiya Hadiza wacce ta bar gidan iyayenta su ke ta neman ta.

Daga bisani dai iyayen nata su ka je hukumar ta Hisba domin ta nemo ma ta ‘yar ta su, inda hukumar ta baza jami’anta suna bin gidajen da ake zarginsu da aikata badala, bincikensu kuma ya gano cewar ta na gidan matar da ake zarginta da yin kawalci, su ka kamo ta da sauran wasu matan har dama ita matar da ake zargin, kuma da zuwan su hukumar aka fara yi musu gwajin cutar HIV.

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya zanta da wani daga cikin ‘yan’uwan samarin da aka kama a gidan inda ya ce, “Wannan ita ce take jan su, saboda kamar yadda aka fada wannan tsohuwa kowa ya na ganinta za ta je ta samu yaran (may be) kila cikin iya magana, kuma wannan yaro sana’arsa ma kafinta ya na taimakawa iyayensa, musamman ma mahaifiyarsa, idan aka je aka gaya ma ta za ta ce ba halinsa ba ne.

Matasan da aka kama a gidan sun nuna nadamar su, kuma su ka ce wannan shi ne karo na karshe ba za su kuma aikatawa ba.

Sai dai wacce ake zargin, ta ce ba za ta yi magana a rediyo ba, inda ta kuma bada hanzarinta da cewar, ita ba kawaliya ba ce kasuwanci ta ke a wannan gida.

Mataimakin Babban Kwamandan hisbar kan al’amuran yau da kullum wanda Malam Tasi’u Ishak ya ce, “Babu shakka duk inda kaga tsohon banza to asali yaron banza ne, saboda haka idan aka samu irin wannan, matakin da za’a dauka shi ne mataki na hukuma, ta yadda za a kai ga alkali, shi kuma alkali ya yi hukuncin da ya dace.”

Ya kuma kara da cewar, “Duk sanda namiji ko mace ya dauki harkar fasikanci sana’a, to ya na kan fadawa cikin garari, saboda haka tabbacin akwai cutar ko babu sai (result) sakamako ya fito, daga nan ne mutum zai san babu, kuma ko mutum yaga babu bai hana anjima ya kamu da cutar ba idan ya ci gaba da yi.”

Wakilin namu ya so jin ta bakin ‘yan matan suma amma sai su ka ki cewa komai.

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending