Connect with us

Labarai

Zamu yiwa masu sha’awar mallakar bindiga lasisi- Rundunar ‘yansanda

Published

on

Rundunar yansandan jihar Katsina karkashin kwamishinan yansandan jihar, CP Sanusi Buba, ta ce ta samu nasarar bindige wasu mutane 2 da sukayi garkuwa da wani mutum mai suna Poul Lawan a karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isa, shi ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da wakilin gidan radiyon Dala Yusuf Nadabo Ismail ya kai jihar.

SP Gambo Isa ya ce” Mun yi musayar wuta da wasu mutane a dajin Jigawar Shawai dake karamar hukumar Dan musa mun kuma samu nasarar harbe wani mai suna Gambo Malajo da wani mai suna Ali Dan Mai Shago wadanda suka sace wata yarinya suka nemi kudin fansa har Naira miliyan biyu”.

Kakakin ya kuma ce” Mun kuma kubutar da wata matashiya wadda aka sace aka boye ta a dajin Barawa dake karamar hukumar Batagarawa. A cikin watanni biyu mun kubutar da mutane da dama sun kuma kama yanfashi da barayin shanu”. A cewar SP Gambo.

Wakilin mu ya kuma tambayi SP Gambo dangane da mallakar bindiga ga farar hula, sai ya ce” A shirye muke mu yiwa mutanen da suke kananan hukumomi 8 lasisin mallakar bindiga domin kare kai tunda dokar kasa ta yadda da hakan, kuma za ka iya harbe duk wani bata gari da yake neman cutar da kai musamman ma har idan ya shigo cikin gidan ka, domin ko addinin ya ba ka damar kare kanka. Kuma kiran mu ga matasa da su rinka shiga aikin kato da gora wato na ‘yan sintiri ko kuma aikin ‘yansandan cikin jama’a na PCRC, kuma ku tabbata kuna zuwa wajen turawan ‘yansanda yankunan ku domin koyon dabarun aiki”.Inji SP Gambo.

A karshe muna kira ga duk wani mai garkuwa da mutane ya mika wuya in kuma an ki ji to ba ka ki gani ba, saboda wannan Karin babu zabi wajen sasanci tsakanin mu da ku”. SP Gambo.

 

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!