Connect with us

Manyan Labarai

Karota ta daure ta kara mana lokaci inji direbobin Adaidaita Sahu

Published

on

Laraba 29 ga watan Janairu ita ce ranar karshe kan wa’adin da hukumar Karota ta baiwa direbobin Adaidaita Sahu, na kammala yin sabuwar rijista, ko kuma ta fara kama su a ranar Alhamis 30 ga watan na Janairu.

Tun a jiya Litinin ne dai shugaban hukumar ta karota Baffa Babba Dan Agundi ya ba da wa’adin kwanaki uku ga direbobin Adaidaita Sahun, a yayin wani taro da su ka gudanar da shugabnnin kungiyar ta ‘yan adaidaita sahu.

Ya na mai cewa, “Ranar Laraba in Allah ya yarda ita ce rana ta karshe na yin rijistar  Adaidaita sahu wanda yanzu haka ina tare da shugabannin Adaidaita sahun, kuma daga ranar Larabar idan an rufe ina fatan wanda bai je yayi rijistar ba zai je ya ajiye Babur dinsa. Don haka mu na fata ga wadanda ba su riga sun karasa rijistarsu ba, to su yi kokari su kara sa daga nan zuwa ranar Laraba wadda ita ce ranar karshe.”

To ko a yau da wa’adin ya rage kwana daya, me ne ne ra’ayin direbobin Adaidaita Sahun? Wakilin mu Abubakar Isma’il ya jiyo mana ra’ayoyin wasu direbobin.

“Ni Allah yaba ni ikon yi, sannan ‘yan uwana wadanda basu yi ba Allah ya ba su ikon yi, to amma mu na neman alfarma ga MD na hukumar Karota, wadanda ba su yi ba a daure a kara masu lokaci. In dai gwamnati ta fito da wani tsari ka yi din ina ganin shi ne mafita domin na yi ne saboda gudun wulakanci. Wannan lambar gwamnati ta na yi ne domin ta samu kudin shiga, gaskiya ni ban yi ba, kuma ra’ayina ne ban yi ba, kira na ga hukumar Karota da take cewa, za ta rufe nan da ranar Alhamis ta tuna akwai masu aure, akwai matasa wadanda yawanci haya su ke karba.”

Wasu direbobin Adaidaita Sahu kenan su ke bayyana ra’ayoyinsu akan wa’adin fara kama su da zai kare daga gobe Laraba idan har ba su yi sabuwar rijista.

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending