Manyan Labarai
Mayankar Abbatuwa za ta yi maganin cutar Lassa- Sarkin Fawa

Sakataren Sarkin Fawar jihar Kano dake mayankar Abbatuwa, Musa Abdulkadir Gudidi, ya bukaci masu yankan dabbobin hakika na suna dama masu yanka don wata bukata, da su ringa kai dabbobin mayankar ana yanka musu don kaucewa kamuwa da cutar zazzbin Lassa.
Musa Abdulkadir Gudidi ya bayyana hakan ne a ganawarsu da gidan rediyon Dala a yau Talata, lokacin da yake tsokaci kan matakan kare kai daga kamuwa da cutar Lassa dama sauran cututtuka daga nama a kasuwar.
Ya kuma ce, “Akwai tarin cututtuka da ake samu daga naman dabbobi wadanda a gida ba za’a iya ganewa ba, har sai an je mayankar inda likitocin da gwamnati ta ware don tabbatar da lafiyar nama zasu tantancewa.”
Ya kuma kara da cewar, “Masu sana’ar fawa a fadin jihar Kano dama Nijeriya baki daya kamata yayi su ringa yin takatsan-tsan da takardun da su ke kunsawa al’umma nama acikinsu don gudun kamuwa da cutar ta zazzabin na Lassa.”
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, Sakataren Sarkin Fawar ya kuma ce, tuni hukumar kasuwar ta dauki matakin yin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a kasuwar da kuma daukan matakan da suka kamata don tabbatar da tsaftar sana’ar ta su tun daga kan lafiyar dabbobin da ake yankawa har zuwa kan naman.

Manyan Labarai
Za’a hukunta duk ma’aikacin Shari’ar da aka samu da laifi – Babbar Jojin Kano

Babbar jojin Kano mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta jaddada cewar kwamitin ladabtarwa na hukumar Shari’a a jihar, zai hukunta duk wani ma’aikaci a tsagin Shari’a matuƙar aka same shi da laifin cin-hanci da rashawa.
Mai Shari’a Dije Aboki ta bayyana hakan ne a yayin taron ƙarawa juna sani wanda hukumar shari’ar ta gudanar ranar Talata, a ɗakin taro na Murtala Muhammad Library da ke Kano.
Taron an shirya shi ne don tunasar da sabbin ma’aikatan Shari’a, akan nauyin da ya hau kan su don mayar da hankali sosai akan batun gujewa cin-hanci da rashawa.
Babbar mai Shari’ar Dije Abdu Aboki, ta bayyana cewar akwai takaddu masu ɗauke da lambobin wayarta da aka liƙe a bangon kotuna, kuma duk wanda aka yi wa ba dai-dai ba zai iya sanar da ita ta kan lambobin kuma za a dauki mataki akan duk ma’aikacin da aka samu da laifi.
Wakilin tashar Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, a yayin taron taron ma’aikatan Shari’a da al’umma da dama ne suka samu damar halarta.

Hangen Dala
Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.
Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.
Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.
Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.
Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.
Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.
Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Hangen Dala
Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su