Connect with us

Labarai

Limamai su fadakar da matasa illar shaye-shaye –Hukumar Shari’a

Published

on

Shugaban sashen yada addinin musulinci a hukumar shari’a ta jihar Kano, Murtala Muhammad Adam, ya gargadi limaman juma’a dasu yawaita yin huduba kan illar shaye-shaye duba da cewar shi ne ummul aba’isin duk wasu ayyukan bata gari da ake yawan samu a tsakanin matasa dama sauran al’umma a wannan lokaci.

Murtala Muhammad Adam, ya yi wannan gargadin ne a yayin wani gangamin tunatarwa da hukumar ta shiryawa limaman karamar hukumar Ungogo a yau Alhamis.

Ya kuma ce” Matukar idan za’a samu nasarar raba al’umma da shaye-shaye, ta hanyar huduba a masallatai dama sauran hanyoyi, to za a samu raguwar aikata laifuka, Shaye-shaye a tsakankanin matasa ya zama ruwan dare, wanda a yanzu lamarin ya munana  sakamakon ya fantsama ya shiga gidan matan aure har suma ba’a barsu a ba ya ba wajen ta’ammali da miyagun kwayoyi”.

“Kuma ina kiran ‘yan uwa musulmai da su dage wajen tallafawa al’ummar musulmai na yin tallafi, da a ce kowane mutum zai rinka zuwa da taimakon Naira (10) ya na bayarwa a masallatai da tuni an wuce matsalolin da marasa karfi da marayu da kuma karatun mata a na tallafa masu ta wannan bangaren”. Inji Murtala Muhammad Adam.

Yayin taron dai limaman masallatan juma’a daban-daban daga karamar hukumar ungogo sun halarci taron wanda ya wakana a dakin taro na cibiyar addinin musulunci.

 

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending