Connect with us

Manyan Labarai

Masu yoyon fitsari sun samu tallafin Akuyoyi

Published

on

Kwamishiniyar mata ta jihar Kano, Dr Zahra’u Muhammad Umar, ta nemi mazaje musamman ma ma’aurata da su rika tausayawa iyalan su wadanda suka kamu da lalurar yoyon fitsari.

Dr. Zahra’u Muhammad Umar, ta yi kiran ne a ya yin da gidauniyar Fistula Foundation ta yi taron ya ye mata masu dauke da lalurar yoyon fitsari kimanin su dari, wanda gidauniyar ta aurar da wasu daga cikin su wasu kuwa suka samu tallafi.

Taron wanda ya gudana a Asibitin yoyon fitsari dake unguwar Gini a karamar hukumar Birni, wanda a ka gudanar da shi a karshen makon da ya gabata.

Tana mai cewa” Tausayawa matan masu dauke da lalurar yoyon fitsarin zai taimaka musu wajen rage damuwar da suke ciki ta lalurar, sakamakon wasu magidantan da zarar matan  sun kamu da cutar sai su fara kyamatar su daga baya kuma sai su rabu da matan dalilin wannan cutar ta yoyon fitsari”.

Ta kuma ce” Mu ma a namu bangaren gwamnatin Kano ta na bakin kokarin ta wajen samawa masu lalurar magani ba tare da gajiyawa ba, duka dai domin ganin an kawar da lalurar”. Inji Dr Zahra’u

Da yake nasa jawabin shugaban gidauniyar ta Fistula Foundation, Mallam Musa Isah, yace ”Duk da cewa kyauta muke yi wa matan magani, amma mafi yawan lokuta mukan fuskanci kalubale daga bangaren mazajen matan, domin kuwa bamu fiye amincewa a yi wa matan nasu magani ba, wanda gaskiya sun fi gwammacewa su je ga bokaye ko kuma ‘yan bori domin nemawa matan magani, wanda hakan yakan ba su matsala daga mazajen su”.

A nasu bangaren wasu da su ka ci gajiyar gidauniyar da su ka zo daga wurare daban-daban sun ce” Wannan ya zama wajibi mu nuna farin cikin mu sakamakon irin wannan abun alherin da a ka yi mana gashi har an ya ye mu”. Inji wasu daga cikin matan da su ka ji gajiya.

Wakilin Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a yayin taron gidauniyar ta rarrabawa matan kayayyakin sana’o’in dogaro da kai, wadanda suka hadar da injin markade,  sana’ar kiwo da dai sauran su.

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending