Connect with us

Manyan Labarai

Mata a rinka zuwa kotu maimakon kashe mazaje

Published

on

Wata mata wadda ta shigar da karar mijinta a gaban kotu ta bukaci a tilasatawa mijin ta ya sake ta.

Matar wadda muka sakaye sunan ta ce” Mijin nawa ya na zalinta ta shi ya san a roki kotu da ta raba auren namu gudun kada wani abu ya je ya dawo. Ta kuma shawarci mata da su rinka kai mazajen su kotu maimakon daukar doka a hannu wadda ta ke kai wa ga da na sa ni”.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa, matar dai ta yi karar mijin ta ne a karamar kotun shari’ar musulinci inda ya dauki lauya a shari’ar wadda a ka ja maganar har zuwa gaban babbar kotun shari’ar musulinci dake Kofar Kudu a jihar Kano, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda a kotun ta raba auren nasu a kan tsarin kul’I a ranar Talatar nan.

Manyan Labarai

Bidiyon da ke yawo an sokawa wani matashi Wuƙa a ciki a Ɗorayi ba gaskiya ba ne – Cewar ƴan sandan Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta umarci baturan ƴan sanda a faɗin jihar Kano, da su riƙe duk wanda yazo karɓar belin ƴan fashi da makamin da ta kama na yankin Ɗorayi ƙarama.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Muhammad Usaini Gumele, ne ya bayyana hakan yayin taron magance matsalar daba dake faruwa a unguwar Dorayi Karama, da ya gudana da yammacin yau Alhamis.

Rundunar ƴan sandan ta jihar Kano ta kuma musanta wani bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta dake nuna cewar ana cakawa wani matashi wuka a unguwar ta Dorayi Karama, wanda ta ce bidiyon ba gaskiya bane.

A nasa jawabin kwamnadan bijilanti na jihar Kano Shehu Muhammad Rabi’u, cewa ya yi masu bibiyar waɗanda aka kama da zargin aikata laifuka kamin kammala bincike na cikin dalilin karuwar matsalar daba da fashi da makami a lokuta da dama.

Da yake nasa jawabin dagacin Dorayi Karama Shehu Umar Sani, ya ce za su bayar da duk wani hadin kai da rundunar ƴan sandan take buƙata wajen kamo duk wanda yake cikin ƴan daba ko fashi da makami.

Rundunar ƴan sandan ta kuma ƙara da cewa za ta fara aikin kota kwana a yankin na Ɗorayi, tare da neman haɗin kan sauran jami’an tsaro dan tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin da ma na jihar Kano baki ɗaya.

A ƴan tsakanin nan ne dai wasu rukunin matasa suka addabi al’ummar yankin na Ɗorayi, inda aka zargi sun yi kan mai uwa dawabi akan mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyin al’umma, bayyana da aka ce sun rarraba takardu kan cewar za su kai harin tare da hana yin sallar Tarawi.

Continue Reading

Manyan Labarai

DPO’s ɗin mu duk wanda ya zo belin ƴan Daba ku riƙeshi – Kwamishinan ƴan sandan Kano.

Published

on

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta samar da rundunar yaƙi da ƴan Daba da ƴan Fashi da makamai, da suke addabar mutane a unguwar Ɗorayi ƙarama, tare da samar da gwangwanin Barkonon tsohuwa guda dubu ɗaya dan fara kakkaɓe ƴan Daba a yankin.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na musamman da suka gudanar da masu ruwa da tsaki na unguwar Ɗorayi, da ya gudana yau a yankin wanda Kwamishinan ya jagoranta, domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin.

CP Gumel, ya kuma umarci baturan ƴan sanda a faɗin jihar Kano, da su riƙe duk wanda yazo karɓar belin ƴan fashi da makamin da ta kama, kamar yadda wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito.

A ƴan tsakanin nan ne dai wasu rukunin matasa suka addabi al’ummar yankin na Ɗorayi, inda aka zargi sun yi kan mai uwa dawabi akan mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyin al’umma, bayyana da aka ce sun rarraba takardu kan cewar za su kai harin tare da hana yin sallar Tarawi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun sami karamar hukumar birni a cikin mawuyacin hali:Hon Bashir Chilla

Published

on

Shugabancin ƙaramar hukumar Birni na riƙo dake nan jihar Kano ya ce bayan karɓa wannan ƙaramar hukumar sun same ta cikin muhuyacin hali, kasancewar yadda sakatariyar take babu gyara babu kuɗi.

Shugaban karamar hukumar na riƙo Hon Bashir Baba Chilla ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na samarwa da ƙaramar hukumar Birni ci gaba.

Chilla ya kara da cewa sun sanya idanu kan ma’aikatan da suke aiki a wajen domin zuwa aiki akan lokaci da kuma gudanar da aiki yadda aka tanada domin sauke hakkin al’umma.

Akwai matsalar huta da wannan sakatariyar take fuskanta ta yadda a kullum takan zama babu huta sakamakon rashin kula da injin da yake bayar da huta,amma kawo wannan lokacin an samu gyara shi, inda yanzu haka huta ta samu a cikin sakatariyar, A cewar Chilla.

Akwai matsalar ƴan kilisa da wannan ƙaramar hukumar take fuskanta, adon haka ya zama wajibi shugabancin ƙaramar hukumar ya dau mataki domin kawo ƙarshen wannan ɓarna da ake yi a yayin hawan kilisar.

Haka kuma muna so musamar da kyakkyawan tsaro a ƙaramar hukumar shiyasa yanzu haka muka kafa wani kwamiti wanda zan sanya idon ko ta kwana musamman a wannan lokaci na ƙaratowar sallah karama.

Muna kira ga iyaye da su sanya idanu kan ƴaƴan su domin kaucewa rikice rikice da ake samu na yau da kullum a wannan ƙaramar hukumar.

Zamu tabbatar mun sanya idanu kan asibitocin mu da suke ƙaramar hukumar Birni domin bayar da kulawar lafiya ga dukkanin al’ummar da suke yankin ƙaramar hukumar.

Akwai tsarin da ƙaramar hukumar Birni tayi wajen bayar da tallafin abinci ga al’ummar ƙaramar hukumar ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf domin rage matsin rayuwa da al’umma suke ciki.

Hon Bashir Baba Chilla ya ce a wannan lokaci Ramadan an sami matsalar ciyarwa a wata santa da take ƙarƙashin sa wanda hakan baiyi daɗi ba kuma cikin ƙanƙanin lokaci aka sami canji, domin gudanar da abin da gwamnati ta tsara.

Ina kira ga al’umma duk abin da zasuyi su kasance sunyi abin su tsakanin su da Allah domin hakki ne da aka ɗorawa mu ku.

Domin wannan tsarin na ciyarwa a buƙatar ya isa ga kowa da kowa musamman bamuƙata da suke faɗin jihar nan.

Continue Reading

Trending