Connect with us

Manyan Labarai

An sace asusun Facebook na hukumar KAROTA

Published

on

Wasu masu kutse da ba’a san ko su wanene ba, sunyi awon gaba da asusun Facebook na hukumar lura da ababan hawa ta jihar Kano wato KAROTA.

Asusun mai suna “Kano Road and Traffic Agency -Karota” yana da mabiya sama da dubu tara, wanda a nan ne hukumar KAROTA take wallafa dukkan bayanan ayyukan ta a kafar Facebook.

Sai dai a safiyar yau Laraba ne, aka ga an fara sanya hotunan wasu mata akan shafin, Wanda hakan ya sanya jama’a suka fara cece kuce akai, musamman a dandalin sada zumunta na Facebook.

Gidan Rediyon Dala yayi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar ta KAROTA, inda ya ce zai kira mu, ba da jimawa ba, amma har izuwa wannan lokaci da muke hada wannan rahoto bamu samu ji daga gareshi ba.

Sai dai wata majiya mai karfi daga hukumar ta KAROTA ta tabbatar mana cewa tabbas an samu masu kutse sun karbe wannan asusun, amma tuni masu ruwa da tsaki akai suka fara kokarin ganin an ceto asusun.

Wannan dai ba shi ne karon Farko da masu kutse suka sace asusun jami’an hukumomi ba a Kano, domin kuwa ko a shekarun baya wasu masu kutse sun taba sace asusun tsohon kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Kano SP. Magaji Musa Majia.

Masana a harkar sabbin kafafan sada zumunta na zamani na ganin cewa da yawa hukumomi a Kano na da sakaci wajen bada muhimmanci da tsaro ga asusun su na kafafan sada zumunta.

Labarai masu alaka:

Bai kamata Karota su rusa wurin kasuwancin mu  ba-‘Yan Kasuwar Farm Center

Karota ta daure ta kara mana lokaci inji direbobin Adaidaita Sahu

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!