Connect with us

Manyan Labarai

Cigaban Ilimi ya rataya a wuyan kowa- Farfesa Fatima

Published

on

Shugabar kungiyar Daliban makarantar horar da malamai ta mata a jihar kano, Farfesa Fatima Muhammad Umar, ta yi kira ga sauran dalibai da su kasance masu taimakawa makarantun da suka kammala karatu, domin tallafawa dalibai da ciyar da harkar ilimi gaba.

Farfesa Fatima Muhammad, ta yi wannan kiran ne yayin zantawarta da Gidan Radiyon Dala, a yau Laraba.

Ta ce, “Bai kamata tsofaffin dalibai su bar iya gwamnati ba a harkar ilimi, domin shi ilimi ba abu bane wanda mutum daya zai dauki nauyi ba akwai bukatar masu hannu da shuni su shigo cikin harkar.”  Inji Farfesa Fatima

Anata jawabin ma’ajin kungiyar A’ishatu Usman Zaharaddin ta ce, “Za su rinka kai ziyara makarantun dan baiwa dalibai darasi musamman akan tarbiya tare da malaman su domin samun tarbiyya a tsakanin dalibai da kuma malaman.”

Wakiliyarmu A’isha Ibrahim Abdul ta rawaito cewa, kungiyar ta samarwa makarantar kujerun zama da rijiyoyin Bohol da kuma Gadajen kwanan dalibai da sauran kayan aiki na karatu.

Manyan Labarai

APC ta dakatar da Dakta Abdullahi Ganduje daga jam’iyyar

Published

on

Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.

Mai bai wa jam’iyyar shawara a ɓangaren shari’a a mazaɓar Ganduje, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Halliru Gwanzo, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai a jihar ta Kano, kamar yadda jaridar online ta Nigerian Triker ta rawaito.

Halliru Gwanzo, ya kuma ce sun ɗauki matakin dakatar da tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin jihar Kano take masa a kan yin badaƙala da kuɗin al’ummar jahar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya yi alƙawarin gyara titin garin Kundila da ke ƙaramar hukumar Shanono

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawari gyara titin da ya taso daga babban titin karamar hukumar Shanono zuwa garin Kundila da ke karamar hukumar.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan yayin ta’aziyyar da ya kai na rasuwar ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono Honorable Halilu Ibrahim Kundila.

Marigayin dai ya rasu ne a makon da ya gabata.

Gwamna Abba Kabir Yusif ya kuma bayyana kaɗuwar sa a lokacin da yaji rasuwar Marigayin, inda ya ce mutum ne mai gaskiya da rukon amana.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Abba Kabir ya kuma ce gwamnatin Jihar Kano za ta dauki nauyin karatun iyalan mamacin daga inda suka tsaya har su kammala karatun nasu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo (Daso) ta rasu

Published

on

Fitacciyar Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Saratu Gidaɗo wadda akafi sani da Daso, ta rasu a yau Talata.

Mijin ƙanwar marigayiya Daso, kuma mai baiwa gwamnan Kano shawara a kan harkokin tafiye-tafiye da shaƙatawa Mustapha Ibrahim Chidari, ne ya tabbatar wa wakilinmu Bashir Sharfaɗi rasuwar ta a ranar Talata.

Ya ce da Asubar yau tayi Sahur, ta koma Bacci, sai dai kuma zuwa wajen ƙarfe 10 na safe aka ga bata fito daga ɗakin ta ba, ko da aka shiga ɗakin ne aka tarar ta rasu.

Mustapha, ya ce za’a yi jana’izar ta da yammacin Talatar nan, da misalin ƙarfe 04:30 a gidanta dake Chiranchi cikin garin Kano.

Marigayiya Daso, guda ce daga cikin fitattun jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wadda ta shafe shekaru a masana’antar.

Continue Reading

Trending