Connect with us

Manyan Labarai

Lokacin kashe wando ga matasa ya wuce- Dan Masanin Kano

Published

on

Dan masanin Kano Alhaji Abdullakadir Yusuf Maitama Sule, ya ja hankalin matasa da su tashi tsaye don nemi na kansu ba wai dogara da aikin gwamnati ba.

Alhaji Abdullakadir ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude wani sabon ofishin sayar da kayan gine-gine dake kan titin Lodge Road a cikin tsakiyar birnin Kano.

Ya ce, “Yanzu lokaci ya wuce da matasa za su rinka bata lokaci suna yin abubuwan da basu dace ba, musamman ma fadawa harkar shaye-shaye, wanda yayi Kamari a wannan lokaci.” Inji Dan masanin Kano

Dan masanin ya kuma yabawa matashin da ya bude wannan shagon, tare dayin kira ga sauran matasa da su jajirce wajen yin sana’o’in dogaro da kai.

A nasa bangaren wanda ya bude shagon na sayar da kayan gine-gine Injiniya Khalifa Rabi’u ce ya yi, “Ya yi wannan kokari ne domin taimakawa kansa da kuma sauran mutane da suke tare da shi, kuma zan yi kokari wajen bunkasa sana’ata domin ciyar da Jihar Kano gaba dama kasa baki daya.”

Matashin ya kuma bukaci gwamnati da ta cigaba da basu hadin kai wajen bunkasa sana’o’in da su ke yi wanda hakan zai taimaka wajen samar da aikin yi ga sauran ‘yan uwansu matasa.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!