Manyan Labarai
Sarkin Hausawa ya magantu a kan hana Achaba a jihar Legas

Maimartaba Sarkin Hausawan Agege a jihar Legas Alhaji Musa Muhammad, ya bayyana cewa akwai lauje cikin nadi kan labaran da ake ta yadawa cewa gwamantin jihar Legas ta hana hausawa yin sana’ar achaba a jihar.
Sarkin ya bayyana hakan ne, da safiyar yau Jumu’a yayin da yake zantawa da wakilin mu Tijjani Adamu a yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Kano.
Inda ya ce” Hakikanin abun da yake faruwa dai shi ne, gwamnatin jihar Legas ta haramta sana’ar achaba da kuma masu Babura masu kafa uku wato Napep a wasu kananan hukumomi 15 dake jihar, amma haramcin bai shafi yankin Agege da Hausawa ke da yawan al’umma ba, da ma sauran yankunan jihar” A cewar sa.
Idan mai karatu bai manta ba dai, gwamantin jihar Legas ta ce ta haramta sana’ar achaba a yankunan ne, saboda magance afkuwar hadura da kuma magance cinkoson ababan hawa a yankunan.
Dokar ta fara aiki ne a ranar Asabar 1 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Izuwa yanzu dai ‘yan sanda a jihar ta Legas sun yi ikirarin kwace Babura har guda 188 da kuma Keke Napep guda 78 tun bayan fara aiki da dokar ta yi.

Manyan Labarai
Jarabawar JAMB: An dakatar da duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025 – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025, domin bai wa ɗaliban da za su rubuta jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB, damar isa cibiyoyin zana jarrabawar a kan lokaci.
Kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Dahir Hashim Muhammad ne ya sanar da hakan, a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Sama’ila Garba Gwammaja ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, an dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin bai wa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ta JAMB, ba tare da wata matsala ba.
“Muna mai tabbatar wa mazauna Kano cewa, dakatarwar duban tsaftar muhallin na wucin gadi ne a iya wannan watan kawai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar muhallin a watan Mayun 2025, “in ji Dr. Ɗahir”
Kwamishinan ya kuma yi kira ga mazauna jihar Kano, da su ba hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci, musamman na ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba.

Manyan Labarai
Babu ɗaga Ƙafa tsakanin mu da Ƴan Daba da masu ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Wayoyin jama’a da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Phone, ta gargaɗi matasan da suke addabar al’umma da faɗan Daba a cikin birnin jihar Kano, da su ƙauracewa hakan domin ba za su saurarawa dukkanin wanda ya faɗa komar su ba.
Kwamandan rundunar tsaron a jihar Kano Inuwa Salisu Sharaɗa, shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, ya ce duk wanda suka kama da laifi musamman ma na faɗan Daba, ko ƙwacen waya ko kuma sha da dillancin kayan maye, za a ɗauki tsattsauran mataki akan sa.
“Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu ƙwacen Wayoyin jama’a, da Faɗan Daba, da kuma masu Sha da dallancin kayan Maye a jihar Kano, kuma duk wanda mu ka kama sai mun miƙa shi gurin da ya dace don ɗaukar Mataki, “in ji Inuwa Sharaɗa”.
Ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya idanu wajen kula akan shige da ficen ƴaƴan su, ta yadda za su zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Manyan Labarai
Za’a hukunta duk ma’aikacin Shari’ar da aka samu da laifi – Babbar Jojin Kano

Babbar jojin Kano mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta jaddada cewar kwamitin ladabtarwa na hukumar Shari’a a jihar, zai hukunta duk wani ma’aikaci a tsagin Shari’a matuƙar aka same shi da laifin cin-hanci da rashawa.
Mai Shari’a Dije Aboki ta bayyana hakan ne a yayin taron ƙarawa juna sani wanda hukumar shari’ar ta gudanar ranar Talata, a ɗakin taro na Murtala Muhammad Library da ke Kano.
Taron an shirya shi ne don tunasar da sabbin ma’aikatan Shari’a, akan nauyin da ya hau kan su don mayar da hankali sosai akan batun gujewa cin-hanci da rashawa.
Babbar mai Shari’ar Dije Abdu Aboki, ta bayyana cewar akwai takaddu masu ɗauke da lambobin wayarta da aka liƙe a bangon kotuna, kuma duk wanda aka yi wa ba dai-dai ba zai iya sanar da ita ta kan lambobin kuma za a dauki mataki akan duk ma’aikacin da aka samu da laifi.
Wakilin tashar Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, a yayin taron taron ma’aikatan Shari’a da al’umma da dama ne suka samu damar halarta.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su