Connect with us

Labarai

Rashin aikin yi ke kawo yawaitar ta’addanci- Dakta Sani Malumfashi                                 

Published

on

Wani Masanin zamantakewar Dan’adam dake jami’ar Bayero a jihar Kano, Dakta Sani Lawan Malumfashi, ya bayyana rashin aikin yi da Talauci a tsakanin al’umma, a matsayin abinda ke haifar da garkuwa da mutane da sauran laifukan fashi da makami.

Dakta Malunfashi, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala, a yau Litinin.

Yana mai cewa, “Samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tallafa musu da jari zai taimaka matuka wajen rage yawaitar garkuwa da mutane da ake samu a jihar Kano.”

Anasa jawabin Kaftin Abdullahi Bakoji, mai ritaya ya ce, “Akwai banbanci a bangaren jihar Katsina, wanda rashin adalci ne ke kawo yawaitar garkuwa da mutanen a jihar.”

Kaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, ya kuma yi kira ga al’umma da su marawa jami’an tsaro baya don ganin an kori dabi’ar garkuwa da mutane a  fadin Nijeriya.

Labarai

Rahoto: Addu’a ce babbar hanyar magance matsalar tsaro – Dagaci

Published

on

Dagacin Sharada Alhaji Iliyasu Mu’azu Sharada ya ce, al’umma su yawaita yin addu’a domin ita ce babbar mafita wajen magance matsalolin rashin tsaro.

Alhaji Iliyasu Mua’azu, ya bayyana hakan ne yayin da wata kungiya mai suna Sharada Foundation ta mika masa na’urar over-over guda takwas a rabawa kungiyar ‘yan sintiri ta Bijilante da ke yankin domin inganta harkokin tsaro.

Saurari Abba Isah Muhammad domin jin cikakken rahoton.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Ana zargin ‘yan ta’adda sun yi wa matashi yankar Rago a Kano

Published

on

Ana zargin wasu matasa a unguwar Danrimi, Rijiyar Lemo da ke karamar hukumar Ungogo, sun shiga dakin wani mutum sun yi masa yankar Rago daga bisani kuma dauke wayar sa.

Marigayin mai suna Shu’aibu Bichi mai sana’ar adaidaita sahu, ‘yan ta’addan da ba a san ko su waye ba sun shiga dakin sa bayan sun lura bai rufe dakin ba, su ka yanka shi, sannan kuma suka dauke wayarsa.

Saurari Abubakar Sabo domin jin cikakken rahoton.

 

 

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Zaman gidan gyaran hali ya sa na daina shaye-shaye – Matashi

Published

on

Kotun majistiret mai lamba 1 da ke Kofar Kudu, wani matashi ya sake gurfana a gaban kotun kan zargin shiga gidan mutane bayan sha kayan maye ya na tsammanin gidan su.

Matashin bayan an karanta masa kunshin tuhumar ya amsa laifin sa, sai dai ya bayyanawa kotun cewar, bai sai ya shiga gidan mutanen ba domin ya yi tunanin gidan su ne.

Domin jin cikakken rahoto saurari Ibrahim Abdullahi Sorondinki.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!