Connect with us

Manyan Labarai

Kotu ta bada belin mawaki a Kano

Published

on

‘Yan majalisar dokokin jihar Kano su biyu suka cika sharudan da a ka sanya dangane da bayar da belin mawaki Buhari Muhammad Kosan waka, wanda hukumar tace fina-finai ta gurfanar da shi, sakamakon fitar da wata waka ba tare da sahalewar hukumar ba, da kuma laifin bata suna da yunkurin tayar da tarzoma.

To sai dai jim kadan bayan cika ka idar kotun majistret mai lamba 72 karkashin mai Sharia Aminu Gabari ta bayyana cewar ba a fahimci turancin da ya yi ba, kawai dai shi ya na cewa Daraktoci 2 daga bangaren shari’a ko bangaren majalisa ko bangaran zartaswa su ne za su gabatar da takardun shaidar biyan haraji na shekaru 3 domin karbar belin sa.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewar, kotun ta ayyana cewar idan Kosan waka ya tsere masu karbar belin za su biya dubu dari biyar.

Labarai

Rahoto: Zaman gidan gyaran hali ya sa na daina shaye-shaye – Matashi

Published

on

Kotun majistiret mai lamba 1 da ke Kofar Kudu, wani matashi ya sake gurfana a gaban kotun kan zargin shiga gidan mutane bayan sha kayan maye ya na tsammanin gidan su.

Matashin bayan an karanta masa kunshin tuhumar ya amsa laifin sa, sai dai ya bayyanawa kotun cewar, bai sai ya shiga gidan mutanen ba domin ya yi tunanin gidan su ne.

Domin jin cikakken rahoto saurari Ibrahim Abdullahi Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Harbi 6 mu ka yi wa Kadar kafin mu kama ta – Baushe

Published

on

Wasu mafarauta mutum biyu sun yi nasarar kama katuwar Kada a wani kududdufi da ke unguwar Jakada, Dorayi babba a karamar hukumar Gwale.

Baushe Liti daya daga cikin wadanda suka kama Kadar ya bayyanawa wakilin mu Tijjani Adamu cewar, sun dauki lokaci suna harbin katuwar Kadar kafin daga bisani su ci nasarar kama ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

#SecureNorth: Mun gaji da salon mulkin Buhari – ‘Yan Najeriya

Published

on

Ƴan Najeriya sun fara kosawa da salon mulkin gwamnatin kasar da suka ce ta yi biris da sha’anin tsaro.

Wannan na zuwa ne yayinda al’amauran tsaro a arewacin kasar ke kara tabarbarewa, a dai-dai lokacin da alhinin mutuwar manoma 43 da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka yi musu yankan rago a jihar Borno.

Al’ummar kasar dai na ganin munin matalsar tsaro na kara ci musu tuwo a kwarya, lamarin da ya sanya da dama daga cikin al’ummar kasar suka fusata, inda suke bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta.

Abinda kuma ke yawo a kafafenn sada zumunta baya ga batun sai Buharin ya sauka daga mulkin kasar, shine batun a sallami hafsoshin tsaro, akan abinda ‘yan Najeriya ke cewa sun gaza magance matsalar tsaro da ke kara kamari musamman, a arewacin kasar.

Haka zalika al’ummar Najeriya sun ce shugaban ya gaza cika musu alkawuran da ya dauka a lokacin da yake neman kujerar shugabancin kasar, a yayinda tsadar rayuwa ke ci musu tuwo a kwarya.

Yanzu haka dai hankulan mazauna arewa maso yamma da ke fama da matsalar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a tashe yake, yayinda mazauna yankin arewa maso gabashin kasar ke cikin tashin hankali.

Tun bayan yankan ragon da aka yiwa manoma a kauyen Zabarmari na jihar Borno ne, hankulan jama’a ya kara karkata, yayinda ake ganin mazauna arewacin kasar na cikin tashin hankali, sakamakon tabarbarewar tsaro.

Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu ana neman wasu daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su, yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin ko shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalar tsaron ko kuma ya sauka daga mulki.

Me ke faruwa a Arewa maso Yamma?

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce manoma 110 ne aka kashe a Zabarmari na jihar Borno, ba 43 ba kamar yadda hukumomin tsaron kasar suka ce.

Majalisar ta bayyana wannan harin a matsayin abu mafi muni da aka yiwa fararen hula, cikin shekarar 2020 a duniya.

A dai-dai lokacin da ake zaman makokin mutuwar manoman ne, kuma rikici ya balle a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutum bakwai, sai kananan yara da suka tsere bayan da wasu na daban suka jikkata.

Bayan kwana guda da barkewar rikicin ne, wasu ‘yan bindiga suka tare hanyar Zaria zuwa garin Kaduna, inda suka jikkata mutane, ko da yake kawo yanzu ba a tabbatar da mutuwar ko da mutum guda ba.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!