Connect with us

Wasanni

Gudunmawar da Kabiru Baleria ya bayar a harkar kwallon kafa

Published

on

Kabiru Umar Baleria an haife shi ne a ranar 5 ga watan Afirilu a jihar Kano shekarar 1972, ya yi makarantar wasanni ta jihar Legas inda ya samu shaida a bangaren masu horaswa a shekarar 2005. Sannan a shekarar 2008 ya kumqa samun shaida a bangaren horasawa a makarantar.
Kafin rasuwar sa, ya samu lasisin horaswa a wurin hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF a shekarar 2014.
Ga jerin kyaututtuka da ya samu kamar haka:

Kabiru Baleria lokacin da yake horaswa a Nijeriya

1 Makarantar wasanni ta kasa dake Gurara a Minna wanda ya samu zinariya.
2 Kofin chalenji wanda a ka yi a jihar Legas a shekarar 1991 ya kuma samu lambar yabo.
3 Kofin King Fahad na kasar Saudia Arabia, ya samu azurfa a shekarar 1993.
4. Gasar wasanni da a ka gudanar a kasar Kamaru mai taken Couped de cameroun cup competition wanda a ka yi a birnin Younde ya kuma samu azurfa a shekarar 1998.
5 Gasar Ecowas ta ‘yan kasa da shekaru 20 ya samu lambar yabo a shekarar 1990.
6 Coca cola F A cup tsohon dan wasa da ya samu lambar yabo a shekarar 2003.
7 Gasar wasannin jami’o’I karo na 22 na Nuga games wanda a ka yi a Nsuka ya samu azurfa a shekarar 2009.
8 Gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 ya samu lambar yabo a shekarar 2015.

Kwarewar sa da ya samu a kai.

1 Mai horaswa kuma dan wasa a kungiyar El Kanemi Warrious fc a shekarar 2000.
2 Mataimakin mai horasawa na Kano Pillars.
3 A shekarar 2009 ya yi aiki da kungiyar kwallon kafa ta jami’ar Bayero dake Kano.
4 Mataimakin mai horaswa na Kano pillars a shekarar 2009/2012.
5 Mataimakin kungiyar Nijeriya ta Golden Eaglet ta ‘yan kasa da shekaru 17 a shekarar 2015.
6 Mataimakin mai horaswa na Nigeria ‘yan kasa da shekaru 20 shekarar 2016.
7 Mai horas da Kano Pillars shekarar 2016/2017.
8 Manajan kungiyar Kano Pillars shekarar 2017/2018.
9. Mukaddashin mai baiwa Kano Pillars shawara a shekarar 2018/2019.
10 Manajan kungiyar Kano Pillars har zuwa lokacin da ya rasu.
Kungiyoyin da ya taka leda.
1 Works golden Stars Fc Kano 1987.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending