Connect with us

Wasanni

Covid-19: An dakatar da gasar kofin M.A Lawal a Kano

Published

on

Shugabanin masu gudanar da wasa na gasar cin kofin Barrisat M.A Lawal sun dakatar da gasar sakamakon cutar coronavirus.

Sanarwar mai kunshe da sa hannun sakataren tsare-tsaren gasar Abdullahi Sharada, ya tabbatar da hakan cewa sakamakon dakatar da kowane wasa a Nijeriya su ma suka dauki wannan matakin gudun kada a samu yaduwar cutar.

Manyan Labarai

Shekaru 16: Leeds United na daf da dawo wa gasar Firimiya

Published

on

A karo na farko tun cikin shekaru 16 kungiyar kwallon kafa ta Leeds United na yunkurin dawo wa gasar Firimiya bayan ragargazar Stoke City da ci 5-0.

Leeds United ta dai fada ajin ‘yan dagaji wato Championship a shekarar 2004 tun a lokacin ba ta sake haurowa ba kawo wannan lokacin sai a wannan karon take kokarin dawo wa gasar Firimiya.

Leeds United yanzu haka ta na jag aba a teburin ajin ‘yan dagaji da maki 81 a cikin wasanni 41 da ta yi inda kungiyar West Brom ke biye mata da maki 80 sai Brentford da maki 75.

Yanzu haka kungiyoyi uku ne a gasar ke hawo wa zuwa gasar Firimiya yayin daga uku a cikin na Firimiya kuma ke fadawa ajin ‘yan dagaji wato Championship.

Continue Reading

Manyan Labarai

 La Liga: Real Betis ta nada Pellegrini a mtsayin kocin ta

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Betis ta nada sabon mai horas da ita Manuel Pellegrini a matsayin kocin ta.

Pellegrini wanda ya taba rike kungiyoyin Mancheste City, Real Madrid, Malaga da kuma West Ham zai jagoranci kungiyar a har zuwa sabuwar kaka mai kamawa.

Manuel Pellegrini mai shekaru 66 dan kasar Chile ya rattaba kwantiragi har zuwa nan da watan Yuni na shekarar 2023.

Pellegrini wanda ya lashe gasar Firimiya a shekarar 2013-14 ya kuma lashe gasar EFL Cup a lokacin da ya yi shekaru uku da Manchester City.

Yanzu haka tuni ya maye gurbin Rubi, wanda a ka sallame shi a watan Yuni ranar 21 sakamakon kayi da ya sha a hannun Athletic Bilbao.

Continue Reading

Manyan Labarai

Golf: Tiger Woods zai fafata a gasar PGA

Published

on

A karo na farko dan wasan kwallon Golf Tiger Woods zai fafata a gasar PGA Tour wanda za a yi wasan a mako mai zuwa.

Zakara har sau 15 a cikin gasar bai samu damar fafata w aba tun a watan Fabrairu tun bayan ciwon baya da ya yi a watan Maris kafin a rufe gasar saboda Corona.

Kwararrun ‘yan wasa na Golf dake kasar Amurka ne za su fafata a gasar ba tare da ‘yan kallo, wanda wasan zai gudana a jihar Ohio ranar 16 da kuma 19 ga watan Yuli.

Ya ce” Na yi rashin abokan burmi na da mu ke fafatawa a gasar, domin na kagu na ga an dawo gasar”. A cewar Tiger mai shekaru 44.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish