Connect with us

Labarai

‘Yan sanda sun cafke wani matashi dake yawo da almakashi

Published

on

Kotun Majestrate mai lamba 49 karkashin mai shari’a Hadiza Abdulrrahman, ta daure wasu matasa biyu, Sama’ila Jafar dan uwa Mai Dile, da kuma Ahmad Ali Bala.

Tunda fari dai ‘yan sandan Sheka ne suka gurfanar da matasan biyu inda aka tuhumi Sama’ila Jafar da laifin shan taba wiwi, domin yin maye, bayan kuma an karanta masa tuhumar da ake masa ne ya amsa, kotun kuma ta yiwa masa daurin watanni Hudu ko kuma ya biya tarar Naira Dubu Goma.

Haka zalika shima matashi Ahmad Ali Bala, an tuhumeshi ne da laifin samun sa da Almakashi, wanda bayan karanta masa kunshin tuhumar da ake yi masa shima ya amsa ba tare da wahalar da shari’a ba, a nan ne kotun ta yi masa daurin watanni Uku ko kuma ya biya tara ta naira Bubu Biyar.

Mai shari’a Hadiza Abdulrahman ta yi umarni ga jami’in gida  ajiya da gyaran hali, Babangida Sani da masu taimaka masa, Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna, da su wuce da su gidan ajiya da  gyaran hali.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya zanta da matasan, wadanda suka bayyana nadamar su a fili, wanda suka ce, matukar suka fita daga halin da suke ciki to za su yi kokari wajen ganin sun gujewa aikata laifi makamancin irin wanda suka yi har ma suka ja hankalin ‘yan uwansu matasa da su kaucewa aikata laifuffuka su zama mutane na gari.

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish