Connect with us

Labarai

Sai an yi adalci a kan yaron da a ka hallaka bayan anyi garkuwa da shi -Ayagi

Published

on

Shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam, Comared A A Haruna Ayagi, ya ce za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin anyi adalci kan zargin garkuwa da wani yaro mai suna Muhusin, wanda bayan anyi garkuwa da shi a ka hallakashi, a yankin karamar hukumar Ungoggo dake nan Kano.

Ayagi ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a yau Juma’a.

Abaya dai rundunar ‘yansandan Kano ta tabbatar da kame mutane hudu da a ke zargin su ne su ka yi garkuwa da Muhusin Murtala, dan Shekaru goma sha uku, dan unguwar Tudun Wada a yankin karamar hukumar Nassarawa,

Haka zalika cikin wadanda a ke zargin sun hadar da Garba Yahaya Umar Magobiri mai shekaru 40 da Usman Ibrahim mai shekaru 19 da kuma Yusif Alkasim mai shekaru 21 tare da Umar Yakubu mai shekara 20.

Haka kuma AA Haruna Ayagi, ya kara da cewar za su bincika lamarin domin ganin an tabbatar da adalci.

Sai dai mahaifin marigayi Muhusin Engineer Murtala Adam Aliyu, ya ce su na bukatar adalci daga hukuma sakamakon raba shi da dansa da a ka yi.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending