Connect with us

Labarai

Covid-19: Gwamnatin ta fara bincike a kan mamatan da su ka rasu a Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya baiwa ma’aikatar lafiya ta jihar umarni gudanar da bincike a kan gawarwakin wadanda su ka rasa rayukan su  a cikin makon da ya gabata.

Sanarwar mai kunshe da sa hannun kwamishinan yada labarai, Kwamrade Muhammad Garba ya sanyawa hannu, ta ce tawagar jami’an lafiya da kuma hukumar dakile cututtuka masu yaduwa (NCDC) sun bazama cikin wasu kananan hukumomi takwasa dake karkashin masarautun Kano domin fara gudanar da bincike a kai.

Ya ce” Bayan da gwamnan Kano ya bada umarni, tuni jami’an lafiya karkashin ma’aikatar lafiya da na NCDC a ka umarce su da su bi iyalan matatan da wajen ganin sun bibiyi sakamakon lafiyar su da a ka yi musu a baya domin tabbatar da musabbabin mutuwar mutanen. Sannan jami’an mu na lafiya a matakin farko mun umarce su da su ci gaba gudanar da ayyukan su a kananan hukumomi 44 domin ganin sun aiwatar da ayyukan su na lafiya duk da ci gaba da yakin da mu ke da wannan cuta ta Covid-19”. Inji Muhammad Garba.

Kwamrade Muhammad Garba, ya kuma shawarci al’umma da su ci gaba bin umarnin kwararru a bangaren lafiya domin kaucewa kamuwa da cutar Covid-19. Sannan kuma ya ce yanzu haka ma’aikatar lafiya ta jihar Kano na kokari wajen samar da magungunan cutar zazzabin cizon sauro, zazzabin Typhoid, sankarau da dai sauran su.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending