Connect with us

Labarai

Covid-19: Sarakuna ku rubanya kokarin da ku ke yi a kan yaki da cutar -Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ga na da sarakunan gargajiya biyar masu daraja ta daya a jihar kan annobar Covid-19.

Yayin ganawar da ta gudana a fadar gwamnatin Kano, Gwamna Ganduje ya nemi sarakunan da su rubanya ayyukan da su ke yi na wayar da kan al’umma kan cutar Corona.

Ya ce”Kamata ya yi sarakunan ku jajirce wajen ilimantar da al’umma, domin bin dokokin jami’an lafiya game da cutar da kuma zuwa wajen gwaji ga wanda a ka gani da alamar cutar”. Ganduje

Da yake jawabi Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero kira ya yi ga al’umma kan su dage wajen neman gafararar ubangiji tare da rika taimakawa marasa karfi a wannan yanayi da a ke ciki.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa mai baiwa Ministan lafiya shawara a kan cutar Corona a Kano, Farfesa Abdussalam Nasidi ya ce cikin sati biyu da zuwan su Kano an samu nasara sai dai akwai bukatar karin gudummuwar sarakunan gargajiyar kan yakar cutar.

Labarai

Masu koyarwa a aji su ci gaba da zama a gida – KSSSMB

Published

on

(more…)

Continue Reading

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish