Connect with us

Labarai

Ba mu shirya cafke El-Rufa’I ba -KAROTA

Published

on

Hukumar KAROTA ta karyata rade-radin da a ke ta yadawa a kafar sada zumunta cewa shugaban hukumar, Baffa Babba Dan Agundi, a lokacin da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya shigo cikin jihar Kano.

Maitaimakawa Babbafa Babba Dan Agundi a kan kafafen yada labarai, Aminu Abba Kwaru a lokacin da ya wallafa a shafin san a sada zumunta wato Facebook.

Ya ce Ba bu wannan batu cewa shugaban hukumar Baffa Babbaf Dan Agundi zai kama gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I a duk lokacin da ya shigo jihar Kano.

Wasu ma su amfani da kafafen sada zumunta ne dai kawai su ke wallafawa a shafin su cewa shugaban hukumar zai kama El-Rufa’I da hannun sa mudin ya shigo jihar Kano.

Wannan batun duka ya biyo bayan furta wasu kalamai da gwamnan jihar Kadunan ya yi cewa da kan sa zai je iyakokin Kano da Kaduna ya je ya tare a ranar Sallah domin ganin ya hana wasu al’ummar jihar Kano shigowa cikin jihar sa a ranar.

Wannan batu dai ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al’ummar jihar Kano da kuma ‘yan jihar Kaduna a shafukan sada zumunta dangane da martanin gwamna El-Rufa’i

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!