Connect with us

Manyan Labarai

Covid-19: Dan wasan Tottenham ya kamu da cutar -Premier League

Published

on

A yayin da a ke tsaka da dawowar gasar Premier an samu wani dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta kasar Ingila dauke da cutar Corona.

Kungiyar ce dai ta tabbatar da hakan a shafin ta cewa an samu dan wasan ta guda daya dauke da kwayar cutar wanda yanzu haka zai killace kansa a gida har na tsawon kwanaki 7.

Sai dai kungiyar ba ta bayyana sunan dan wasan ba duk da cewa shi ne a yanzu da a ka samu a cikin ‘yan wasa 1,197 tare da ma’aikata da a ka yi wa gwajin cutar a cikin kwanakin nan.

Kididigar ta nuna cewa a cikin ‘yan wasa 5,079 da a ka yiwa gwajin cutar an samu 13 daga cikin su dauke da cutar.

A duk cikin makwanni biyu a kan yi wa ‘yan wasa tare da ma’aikatan kungiyoyin gasar Premier gwajin cutar ta Corona sakamakon dawowa gasar da za a yi a ranar 17 ga watan nan.

Labarai

Sha’iri ya auri mata ba tare da sanin mahaifin ta ba

Published

on

Wani fitaccen sha’iri mai gudanar da majalisi a jihar Kano a na zargin ya angwance da amaryar sa ba tare da sanin iyayen ta ba.

Sha’irin ya gurfana ne a gaban kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a unguwar Goran Dutse, inda a ke zargin sha’irin ya hada kai da mahaifiyar Amaryar sa a ka daura ma su aure ba tare da sanin waliyin ta ba, wanda ta kai har ta tare a gidan sa, yayin da kuma saura kwanaki kadan a yi bikin ta da wani mutum daban.

Sai dai Ango da Amaryar su na zaman auren ne mahaifin ta da ya ke baya gari, ya dawo ya ji labarin auren su, nan kuma take ya garzaya tare da waliyin Amarya gidan, domin tabbatar da al’amarin, daga bisani su ka shigar da kara a kotun shar’ar musulunci.

Tuni dai kotun ta zauna ta saurari karar, kuma lauyan wanda a ke zargi ya gabatar da da’awar cewar, mahaifin ta ba shi da hurumin da zai yi mata walicci, saboda tsawon lokaci ba shi yake ciyar da ita ba, hasali ma kuma kula da ita ba shi ne ba, domin haka hakkin walicci ya tashi a kan sa.

A nasa bangaren, shima lauyan masu kara ya ce,” Sai dai kotun ta sanya Amaryar a igiyar wakafi tun da akwai shakku a kan auren a na cikin shari’a”.

Kazalika, kotun ta sanya Amaryar a hannun wakafi, inda a ka damka ta a hannun yayan ta, kuma babu batun ci gaba da zama a gidan sha’irin, har sai an gama kammala zaman kotu.

Kotun kuma ta umarci Angon ya dauko Amaryar ta sa da hannun sa ya kawo ta wajen yayan ta, domin ta ci gaba da zama a hannun sa.

Continue Reading

Labarai

Kano: ‘Yan Bijilante sun tafi yajin aiki

Published

on

Kungiyar ‘yan sintiri ta bijilante da ke garin Zawaciki a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, sun tafi yajin aikin bayar da tsaro na kwanaki biyar saboda sabanin da su ka samu tsakanin su da matasan unguwar.

Al’amarin ya faru ne a masallacin Idi da ke Zawaciki lokacin bikin sallah babba, inda ‘yan bijilanten su ka rufe ofishin su wanda su ke gudanar da aikin bayar da tsaro a unguwar.

Nuhu Salisu Zawaciki, mataimakin shugaban bijilante na garin Zawaciki a zantawar sa da gidan rediyon Dala ya ce, “Duk shekara kungiyar mu, mu na samun abokan aiki ma su zuwa su bamu gudunmawa, kuma karfe shida mu ke busa ‘kusur kowa ya tafi, saboda bata gari ma su shaye-shaye, to sabanin da a ka samu shi ne akwai baki wadanda ba su san yadda dokar wajen take ba”.

Ya kuma ce, “Iyayen kungiya sun shiga cikin al’amarin, an samu zama na daya da na biyu, a na samun ‘yan kura-kurai, shi yasa ma mu ka nemo shugabanni na karamar hukuma domin bamu shawara, saboda kaucewa samun matsala. Jin kirin rashin zama ne ya sanya mu ka rufe ofishin mu, duk wadanda a ka samu matsala an nemo su an samu fahimtar juna, inda a ke da kuskure za a gyara. Bangaren mu akwai wanda ya samu rauni, su ma kuma a bangaren su akwai wanda ya samu rauni”. A cewar Nuhu Salisu

A nasa bangare, wani daya daga cikin ‘yan kungiyar ci gaban garin Zawaciki, mai suna Mu’azzam Muhammad, ya ce, “Ba mu ji dadin abun da ya faru ba, domin tafiyar ‘yan bilante din an samu haurawa gidajen mutane, da kuma sace-sace, mu na fatan a nan gaba hakan bai sake faruwa ba”. Inji Mu’azzam Muhammad

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawato cewa, Nuhu Salisu Zawaciki, ya kuma yi yi kira ga al’umma da ‘yan kungiyar bijilante a hada kai domin kawo ci gaban unguwa.

Continue Reading

Labarai

Za a ci gaba da shari’ar matashin da ya kashe abokin sa

Published

on

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 8 karkashin mai shari’a, Usman Na Abba ta sanya ranar 12 ga wata, domin fara sauraron karar wani matashi wanda gwamnatin Kano ta ke zargin sA da laifin kisan kai.

Gwamnatin jIhar Kano ta na zargin matashin Bashir Abdullahi Bachirawa da laifin kisan kai karkashin kundin sashi na 221.

Kunshin zargin ya bayyana cewar matashin ya yi amfani da Adda ya sarewa marigayi, Ibrahim Umar kafada ya kuma farke masa ciki.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da lauyan gwamnati, Lamido Soron Dinki, inda ya ce“Sun taba fada sun sari juna, amma daga baya ya jawo marigayin daga cikin gidan su, ya sassare shi, kuma hakan laifi ne babba na sashi 221 (A) wato A cikin baka, a sarewa mutum ‘yan yatsu a fasa masa tumbin sa wannan ya nuna cewa da gaske ya yi wannan danyen aikin, kuma za mu yi iya kokarin mu, domin an biwa marigayi hakin sa”. inji Barista ALamido.

Duk wani yunkuri domin ji daga bakin wanda a ke zargin matashin, Abdullahi Bachirawa abun ya faskara, amma duk da haka wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya hango matashin a tsare a cikin kotun.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish