Connect with us

Wasanni

An amince za a rinka yin sauyin ‘yan wasa biyar a cikin fili

Published

on

Kungiyoyin gasar Premier ta kasar Ingila za su iya yin canjin ‘yan wasa har guda biyar a cikin fili a yayin da a ke tsaka da wasa har sai an kamala gasar a wannan kaka.

Yanzu haka dai kungiyoyin na da damar fitar da sunayen ‘yan wasa tara maimakon ‘yan wasa bakwai a baya.

An dai baiwa kungiyoyin umarnin kara ‘yan wasan ne domin kare lafiyar ‘yan wasan a lokacin da a ka dawo gasar a ranar 17 ga watan Yuni.Top of Form

 

Wasanni

Pirlo: An daura kwarya a gurbin ta – Mancini

Published

on

Tsohon kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce sabon kocin Juventus Andrea Pirlo, ya yi matukar sa a da ya fara aikin horaswa a rayuwar sa da kungiyar Juventus.

Macini na kalaman ne lokacin da Pirlo ya zama kocin Juventus a ranar Asabar bayan da a ka karawa Maurizio Sarri wuta.

Ya ce”Pirlo ya yi nasara a rayuwar sa, saboda ya fara da babbar kungiya, kuma hakan zai zama babban kalubale a shekarar farkon sa, ko saboda ban fara koyar da manyan kungiyoyi ba ne, sakamakon na fara da Fiorentina”. Inji Mancini.

Continue Reading

Wasanni

Manchester City ta yi babban kamu

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City bangaren mata, ta dauki ‘yar wasan tsakiyar kasar Amurka, Sam Mewis.

Mewis wadda ta takawa kasar ta leda ta Amurka har sau 67, kuma ta na daga cikin wadda ta tallafa a su ka dauki gasar cin kofin duniya ta mata a kakar bara bayan da su ka samu nasara a kan kasar Netherlands da ci 2-0 a birnin Lyon ta kasar Faransa.

Yar wasan mai shekaru 27 ta bar kungiyar ta ta North Carolina Courage daga ajin kwararru zuwa kungiyar Manchester City.

Ta ce”Wannan babbar dam ace a gare ni, kuma na ji dadin kasancewa ta da na samu kai na a kungiyar Manchester City”. Inji Mewis.

Wannan dai ita ce ‘yar wasa ta biyu bayan da ta kungiyar ta dauki ‘yar wasan gabar kasar Ingila, Chloe Kelly daga Everton.

Continue Reading

Wasanni

Dortmund: Sancho zama daram a kungiyar – Zorc

Published

on

Daraktan wasannin kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Michael Zorc ya tabbatar da cewa dan wasan gaban kasar Ingila, Jadon Sancho zai ci gaba da zama da kungiyar har zuwa kakar gaba.

Dan wasan mai shekaru 20 yanzu haka ya na daga cikin ‘yan wasan kungiyar Dortmund da za su shiga sansanin horaswa a kasar Switzerland a wannan makon.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Dortumnd ta kawo karshe wa’adin da ta bayar a kan dan wasa Sancho wajen yarjejeniyar da kungiyar Manchester United.

Ya ce“Mu na bukatar dan wasan mu Jadon Sancho a wannan kakar matuka gaya, domin kuwa a kakar bara mun kara masa albashin sa, sakamakon kokarin da ya yi, wanda mu ka kara masa kwantiragi har nan da zuwa kakar 2023”. Inji Zorc.

Dortmund ta na bukatar kudi Fam miliyan100 a kan dan wasan ta Sancho, wanda a baya ta sayi dan wasan a kan kudi Fam miliyan 10 daga kungiyar Manchester City a shekarar 2017.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish