Connect with us

Labarai

Mu rubanya addu’a a kan halin da Nijeriya ke ciki- Liman

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Abdullahi Bin Mas’ud dake unguwar Kabuga ‘yan Azara, Malam Zakariya Abubakar ya ce, hakuri shi ne babban abinda al’umma ya kamata su yi a wannan lokaci da aka fi watanni hudu ana fama da cutar Corona, da ta haddasa yunwa da karayar arziki, sai kuma kashe-kashen mutane da ake yi a wasu daga cikin jihohin arewa.

Malam Zakariya ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gabatar a masallacin na Abdullahi Bin Mas’ud.

Ya na mai cewa, “Allah Ya umarce mu da mu yi hakuri, kuma dama ya ce, zai jarrabi bawa a kan abubuwa guda biyar, tsoro, yunwa, karayar tattalin arziki, noma, da kuma kashe-kashen rayuka, sai kuma a yi wa ma su hakuri bushara, wadanda idan ya jarabce su za su ce, inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”. A cewar Malam Zakariya.

Ya kara da cewa, “Abun da a ke bukata wajen al’umma a yanzu shi ne hakuri a bisa wannan masifa, mu yi hakuri a kan ibada, da kaddara, sannan mu koma zuwa ga Allah, kuma kada mu yi fushi”. Inji Liman

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewar, Malam Zakariya ya kuma ja hankalin shugabanni akan rike amanar al’umma, wajen tsaron Najeriya, domin dakile kashe-kashen da ake fama da shi a halin yanzu.

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Labarai

Iyaye su dora ‘ya’yan su a kan koyarwar addini

Published

on

Limamin masallacin juma’a na unguwar Kabuga ‘Yan Azara, Malam Abubakar Shua’aibu Dorayi ya ce, iyaye su rinka bibiyar alkur’ani da hadisi domin tsinto misalai da hanyoyin tarbiyar ‘ya’yan su.

Limamin ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a masallacin a Juma’ar nan.

Ya na mai cewa, “Annabi ya hore mu a duk lokacin da za mu yi aure mu auri mai tarbiya. Idan kuma yaro ya girma a saba masa da ambaton Allah, tare da nuna masa abun da Allah yake so da wanda baya so, wannan zai sa ya tashi ya na girmama umarni da hanin manzon Allah, kuma a koya masa kadaita Allah”. Inji Malam Abubakar Dorayi.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewa, limamin ya kuma ja hankalin iyaye da su zamo makarantar ‘ya’yan su a gida, wajen koya mu su addu’a a duk abun da za su gudanar.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish