Connect with us

Manyan Labarai

La Liga: Kotu ta umarci Neymar ya biya Barcelon Euro miliyan 6.7

Published

on

Kotu a kasar Andalus ta yanke hukunci a kan dan wasa Neymar da ya biya tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona euro miliyan 6.6 kwatankacin Fam miliyan 6.7.

Dan wasan gaban kasar Brazil kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain kungiyar Barcelona na bin dan wasan bashin kudi har Euro miliyan 43.6 na kudin rarar da ta ke baiwa dan wasan wanda ya tafi da su tun a watan Agusta na shekarar 2017.

Sai dai kotun ta ce dan wasan mai shekaru 28 zai iya daukaka kara har idan bai amince da wannan batun hukuncin ba. Amma kuma dan wasan ya kai korafi wurin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA bayan da Barcelona ta ki biyan sa kudin sa Euro miliyan 222 kwatankwacin Fam miliyan 200 a lokacin da ya bar kungiyar a shekarar 2017.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ce ba za ta yanke hukunci ko daukar mataki ba, amma ta barwa kotun wannan lamarin.

Labarai

Mu godewa Allah a kan jarabawar da ya dora mana – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Madina Sheikh Aliyu Abdul Rahman Al Hudaifyi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar yin hakuri duba da yadda Allah ke jarrabar su da ibtila’i daban-daban.

Sheikh Hudaifyi ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a dake zuwa kai tsaye a tashar Dala wanda Malama Maryam Abubakar take fassara wa.

Ya ce” Kamata al’ummar musulmi su rinka yin godiya ga Ubangiji a dukkanin jarrabawar da Allah ya jarrabe su da ita, duk mutumin da yake hakuri to Allah zai ba shi lada mai yawa”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Aliyu na cewa ya kamata mutane su dage da addu’o’in samun sauki a dukkannin al’amuran rayuwa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Milan Baros zai jingine takalman sa

Published

on

Tsohon dan wasan gaban kungiyar Liverpool Milan Baros ya ce zai jingine takalman sa daga harkokin kwallon kafa a karshen kakar nan.

Dan wasan dan kasar Jamhuriyar Czech wanda ya lashe gasar Champions League eda Liverpool a shekarar 2005 bayan da ya karbi kyautar takalmi na Golden Boot a gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa a shekarar 2004 wanda kasar sa ta kai bantan ta a wasan daf da na kusa da na karshe.

Milan Baros mai shekaru 38 yanzu haka ya na taka leda a kungiyar Banik Ostrava ta kasar Jamhuriyar Czech.

Ya ce” kai na ya na son wasan amma gangar jiki na ba ta so, dole ne in tsayar da wasan haka sakamakon rauni da na ke fama da shi a gwiwa ta”. Baros.

Baros ya taka leda da kungiyoyin Aston Villa da Portsmouth wanda kuma ya lashe gasar FA Cup a shekarar 2008. Ya kuma taka leda a Galatasaray ta kasar Turkiyya da Lyon da kuma Antalyaspor sannan ya komar kasar sa a shekarar 2014.

A shekarar 2012 ne Milan Baros ya rataye takalman sa a kasar sa s shekara 2012.

Continue Reading

Labarai

Tun da ba zuwa aikin Hajji ku taimakawa masu da’awa – Liman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ihya’us Sunnah da ke kofar Nasarawa, Malam Anas Abbas Ibrahim ya ce, Tun da a bana ba a samu damar zuwa aikin Hajji da Umara ba, kamata ya yi masu hali su tallafawa kungioyi da kuma al’ummar da su ke fita wa’azi na musuluntar da wadanda su ke ba musulmai ba.

Malam Anas Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a hudubar da ya gudanar a Juma’ar nan.

Ya ce, “Manzon Allah (S.W.A) an taba hana shi ya yi aikin Umara, wanda hakan ya jawo a ka yi sulhu  a Hudaibiya, bayan anyi sulhun ya hakura, daga nan shi da Sahabban sa su ka himmatu domin jawo mutane su shigo musulunci, manzon Allah (S.W.A) da kan sa ya rubuta wasiku ya aikawa sarakunan duniya, kamar sarkin Farisa da kuma sarkin Rum”.

Malam Anas ya kara da cewa, “A shekarar da a ka yi sulhun ne kuma wadanda su ka shiga musuluncin sun ninka wadanda su ka shiga gabanin haka”. A cewar Malam Anas Abbas

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa, Malam Anas ya kuma ja hankalin samarin da su ke hawa dandalin sada zumunta, su yi kokarin yada abubuwa kyayawa na musulunci tare da kiran mutane zuwa musulunci.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish