Connect with us

Manyan Labarai

Birmingham: Bellingham zai rattaba kwantiragi a Dortmund

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Birmingham City dake kasar Ingila, Jude Bellingham ya tafi kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund dake kasar Jamus domin a yi masa gwajin lafiyar a kungiyar.

A mako mai kamawa ne a ke sa ran dan wasan zai rattaba kwantiragi a kungiyar. A ranar Alhamis ne dai dan wasan ya yi tattaki zuwa kasar Jamus wanda yanzu haka ya na masaukin sa, duk da cewa dan wasan kasar Ingilan wasu kungiyoyi na neman sa ciki harda Manchester United.

Sai dai Burussia Dortmund ta zama kungiya mai rainon kananan ‘yan wasa duk da cewa yanzu haka akwai dan wasan kasar Ingila Jardon Sancho da sauran su.

Bellingham ya kafa tarihi a kungiyar Birmingham a shekarar 2019 cikin watan Agusta wanda ya karya tarihin dan wasan kasar Ingila Trevor Francis a matsayin dan wasa mafi kankanta a kungiyar mai shekaru 16 da kwanaki 38. Sannan ya kuma zura kwallo a wasan san a farko a kungiyar wanda su ka doke Stoke City.

Manyan Labarai

Ƙarancin wutar lantarki da yanayin Zafi na bamu matsala yayin aiki – Hukumar kula da asibia asibitocin Kano – Dr. Mansur Nagoda

Published

on

Hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano, ta ce zafin da ake fama dashi a yanzu, da kuma ɗaukar zafin injinan su bisa yanayin rashin wutar lantarki, shi dalilin da ya sa ake samun matsala, wajan bada kulawa ga mata masu haihuwa, da waɗanda za’a yiwa Tiyata a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke jihar.

Shugaban hukumar dake kula da asibitocin ta jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana wa gidan Rediyon Dala FM, hakan a ranar Asabar.

Nagoda, ya kuma ce a mafi yawan lokuta idan aka shiga da mutum Tiyata, musamman ma mace aka fito da ita ba’ayi ba, haka na da nasaba ne da rashin lafiya, ko kuma ba zata iya ɗaukar iskar baccin da ake bayarwa ba.

A cewar sa, “Da yawan mutane basa yi mana uzuri game da halin da ake ciki na rashin wutar lantarki duk da kasancewar suna zagaya asibitoci, domin tabbatar da marasa lafiya sun samu kulawar data dace, “inji Nagoda”.

Ya kuma ce bangaren duba lafiyar Yara na ɗaya daga cikin wuraren da ake samun cinkoso, baya ga kuma rashin lafiya da ake fama ita a yanzu.

A karshe hukumar ta ce zuwan gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ɗauki likitoci sama da 250, inda aka rarraba su guraren daban-daban domin gudanar da aiki, kuma ƙofar hukumar a buɗe take ga duk mai Korafi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu ta bada umarni ga jami’an tsaro da hukumar Hisbah kan su dakatar da kama Mansura Isah

Published

on

Babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai Shari’a Abdullahi Liman, ta takadar da hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sanda da kuma mataimakin babban Sifeton ƴan sandan kasar nan daga kama Mansura Isa.

Mai Shari’a Liman ya ayyana cewar ya yi hani ga waɗanda akayi karar ko ƴan korensu ko wakilansu, ko kuma wasu masu aiki amadadinsu daga kamawa ko tsorataswa ko gayyata har zuwa lokacin da za’a saurari kowane ɓangaren.

Wannan umarni dai ya samu ne a cikin wata ƙara mai lamba 159/2024, wadda Mansura Isah ta shigar tana karar hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano.

Kotun ta sanya ranar 15 ga wannan watan dan sauraron kowane bangare a shari’ar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Zamu farfaɗo da masana’antun ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano – Kwamishina

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta farfaɗo da masana’antun yin saƙa na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar nan, domin samawa matasa aiki ta yadda za su dogara da kansu.

Kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ne ya bayyana hakan, yayin da ya ziyarci masana’antar saƙar kayayyaki ta ƙaramar hukumar Kura yau Laraba, domin duba halin da take ciki tare da duba yadda za’a farfaɗo da ita daga dogon suman da ta yi.

Tun dai a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a shekarar 2014, ne ya samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin Kano da ta ganata ta yi watsi da masana’anatar.

Yayin duba masana’antar Kwamishinan cikinki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kuma bada tabbacin farfaɗo da masana’antar yin saƙar ta ƙaramar hukumar Kura da ma na faɗin jihar nan, domin samawa matasa ayyukan yi.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani babban sakataren ma’aikatar ciniki da masana’antu na jihar Kano, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, farfaɗo da masana’antar ta Kura, na zuwa ne bisa ƙokarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, domin samawa matasa ayyukan yi.

Ya kuma ce yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da masana’antar tsawon lokaci, a yanzu gwamnatin su za ta yi duk mai yiyuwa, domin ganin an ta ci gaba da aiki ka’in da na’in.

Tun dai a shekarar 2014 ne aka samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da aikin, lamarin da ya sa aikin ya tsaya cak, inda gwamnatin Kano mai ci a yanzu ta ce za ta farfaɗo da ita domin samawa matasa aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Continue Reading

Trending