Connect with us

Labarai

Kano: Za a fara binciken kamfanin da ya kulle ma’aikata a lokacin kulle

Published

on

An nemi majalisar dokokin jihar Kano da ta kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike a kan wani kamfanin shinkafa da ya rufe ma’aikata.

Dan majalisa daga yankin karamar hukumar Kumbotso, Mudassir Ibrahim Zawaciki, ne ya gabatar da ƙudurin gaggawar, kan bukatar majalisar ta kafa Kwamitin binciken yadda kamfanin na shinkafa ya tsare ma’aikatansa har tsawon watanni su na masa aiki a lokacin dokar kulle.

Da yake gabatar da ƙudurin Alhaji Mudassir Ibrahim Zawaciki, ya ce wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin sun miƙa masa ƙorafin cewa, kamfanin ya fara korar wasu daga cikin su daga aikin, wanda hakan ya saba da yarjejeniyar da suka kulla a baya.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne wani kamfanin shinkafa a jihar Kano ya kulle ma’aikatansa har tsawon loakci suna masa aiki, a dai-dai lokacin da ake dokar kullen yaki da annobar Covid-19.

Dan majalisar ya ce ya kamata majalisar ta gudanar da bincike kan wannan kamfanin shinkafa, a kuma kwatowa wadancan mutane hakkokinsu, la’akari da yadda suka dauki tsawon lokaci su na masa aiki, amma kuma lokaci guda an fara sallamar wasu daga cikinsu.

A wani labarin kuma majalisar dokokin ta Kano, ta buƙaci gwamnatin jihar da ta samar da wutar lantarki a garin Ɗan-Amale zuwa Garun-Madadi da ya haɗe da garin ‘Yan Guruza dukkan su a mazaɓar Madidi da ke yankin ƙaramar hukumar Gwarzo.

Hakan ya biyo bayan ƙudurin da dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwarzo Alhaji Yunusa Haruna Ƙayyu ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.

Da yake gabatar da ƙudurin dan majalisr ya ce, samar da wutar a yankin abu ne mai matuƙar muhimmanci kuma zai taimaka wa mazauna yankin.

“Ko da yake tun a baya majalisa ta 6 ta miƙa buƙatar a fara aikin amma sai dan kwangilar ya dakatar da aikin bayan aikin ya yi nisa”. In ji shi

Hakan  kuma majalisar ta buƙaci gwamnatin Kano da ta yi amfani da wani ɓangare na kamfanin samar da taki na jihar Kano KASCO, wajen ƙara gine-gine a kwalejin Fasaha dake garin Kachako.

Majalisar ta buƙaci hakan ne bisa ƙudurin da mamba mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai Alhaji Musa Ali Kachaco ya gabatar.

Ɗan majalisr na Takai, ya ce, samar da ƙarin gine-ginen zai taimaka wajen ƙara bunƙasa harkokin ilimi da rage zaman kashe wanod a tsakanin matasan jihar Kano.

Shima dan majalisa mai wakiltar Ƙaraye, Alhaji Nassiru Abdullahi Dutsen Amare ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin jihar Kano da ta gina Titin da ya tashi daga Kwanar Kafi zuwa Nassarawa zuwa Ƙawara da Gidan Alhaji Ɗan-Ango har zuwa Salihawa duk a ƙaramar hukumar Ƙaraye.

 

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending