Connect with us

Labarai

Lokutan da za a yi Sallar Idi a masallatan Kano

Published

on

Lokutan Sallar Idi Babba da za a gudanar a safiyar ranar Juma’a a wasu daga cikin masallatan Juma’a dake jihar Kano.

Masallacin Juma’a na Ibadur Rahaman Tudun Yola layin Attahiru Jega, za a yi sallar Idi da karfe 7:45 na safiya a harabar Masallacin dake Tudun Yola GRA layin Farfesa Attahiru Jega.

Masallacin idi na garin ‘Yankusa a karamar hukumar Kumbotso za ayi Sallah da karfe 8: 00 na safiya

Masjid Sahaba Kundila Maiduguri Road Kano, za a yi Sallar Idi karfe 8:15.

Masallacin Juma’a, (JIBWIS) Wailari, filin Makarantar Wailari Special Pprimary School za a yi tayar da Sallah karfe 8:30.

Masallacin Idi na garin Durba dake karamar hukumar Kibiya za ayi Sallah karfe 8:45 a filin Idi na garin Durba.

Masallacin Jumu’a na Uhud Na’ibawa Zaria Road za a yi Sallah da karfe 8:30.

Masallacin Abubakar Sadeeq dake Dantamashe A Zangon Gabas za a yi Sallah da 8:00 a karamar hukumar Ungogo.

Garin Dandalama dake karamar hukumar Dawakin Tofa za agudanar da sallar idi babba a ranar Juma’a da misalin karfe 8 a filin makarantar Primary dake garin Dandalama.

Masallacin Bilal dake Karkasara Tarauni za a yi Sallah da karfe 8:00.

Masallacin Abdullahi bin Umar Shekar Mai Daki karfe 8:15.

Masallacin Juma’a na Mariri dake karamar hukumar Kumbotso za a yi sallah 8:15.

Masallacin Nurul Anwar Kwaciri karfe 8:30.

Masallacin Juma’a na Sabilur Rashad dake Ibrahim Umar Street, Hausawa Zoo Road, Za a tayar da Sallah karfe 7:45 na safiya.

Masallacin Jumma’a na ZHERA dake rukunin gidajen Kundila Zoo Road, Za a tayar da Sallah karfe 8 na safe.

Masallacin Juma’a na Sheikh Ibrahim A Ramadan Tudun Nufawa karfe 8:15.

Masallacin Juma’a na Kanwa Madobi karfe 8:00.

Masallacin Juma’a na Bechi Kumbotso karfe 8:30.

Masallacin Juma’a na garin Kumbotso za a yi sallah karfe 8:30.

Masallacin Juma’a na Mariya Sunusi Dan Tata dake Danladi Na Sidi karfe 8:00.

Masallacin Juma’a na Ansaruldin karfe 8:00.

Masallacin Sheikh Ibrahim Inyas Gadon Kaya 8:15.

Masallacin Juma’a na Izala dake ‘Yan Shana Kumbotso 8:30.

Masallacin Mash Arul Haram dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbots za ayi sallah da karfe 8:00.

Masallacin Jauma’a na Abubakar Sadik dake Gwammaja kan titin Tagwayan gida karkashin Liman, Alkali Halhalatul Khuza’i karfe 8:00.

Masallacin Juma’a na Ado Bayero dake garin Ja’en a karamar hukumar Gwale 8:00.

Masallacin Juma’a na Mallam Abubakar Dan Tsakuwa dake Ja’en Ring Road a karamar hukumar Gwale karfe 8:30.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending