Connect with us

Labarai

Ranar abota ta duniya: Mutum zai iya gyara rayuwar abokin sa – Malam Nuhu

Published

on

Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 30 ga watan Yulin ko wace shekara a matsayin ranar abota ta duniya, da nufin wayar da kai da kuma karfafa gwiwar zaman lafiya da farin ciki da kuma hadin kai a tsakanin al’umma.

Haka zalika abokai a sassa daban-daban na duniya kan aika sakonnin fatan alkairi ga abokan su da kuma musayar kyaututtuka na musamman a tsakanin su, tare da tabbatar da kyakkyawar alaka a tsakanin kabilu daban-daban ta hanyar abota.

Bikin ranar  kan mayar da hankali wajen ganin an sanya matasa a harkokin shugabanci ta hanyar karfafa alaka a tsakanin kabilu da kasashe daban-daban, ba tare da yin la’akari da yare ko kabila ko kasa ba.

Wani malami a sashen nazarin ilimin zamantakewar dan adam da ke jami’ar Bayero a nan Kano Dakta Aminu Sabo Dambazau, ya ce, “Akwai dalilai masu yawa da ke sanya mutane kulla alaka ta abota a tsakanin su da wasu”.

Ya kuma ce, “Abota ta na dorewa ne matukar akwai gaskiya da fahimtar juna da kuma taimakekeniya a tsakanin abokai, dabi’a ce ta dan adam ta bukatar wanda zai yi mu’amala da su, kasancewar babu wanda zai iya yin rayuwa shi kadai”. A cewar Dakta Aminu Sabo Dambazau

A na sa bangaren, wani malamin addinin musulunci Malam Nuhu Muhammad Tukuntawa, ya ce, “Abokai na tasiri sosai wajen gyara rayuwar abokan su idan a ka yi dacen samun abokai na gari”. Inji Malam Nuhu Muhammad

Malamin ya kuma yi kira ga iyaye da su rinka sanya ido kan irin abokan da ‘ya’yayen su ke mu’amula da su domin kaucewa yin alaka da gurbatattun abokai.

 

 

 

 

Labarai

Za mu daga likafar sababbin asibitocin masarautun Kano – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta daga likafar sababbin asibitocin masarautun Kano domin ganin sun taimaka wajen rage cunkoso a asibitocin birni dake cikin birnin Kano.

Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin da yake duba yadda aikin daga likafar asibitin Rano ke gudana a yankin.

Ya ce”Asibitin masarautar ta Rano wanda a baya a ke daukar gadaje dari, yanzu zai rinka daukar gadaje dari hudu tare da sabon asibitin idanu dana kula da lafiyar hakora da bangaren gwaje-gwaje a dukannin asibitocin da sauran su, domin haka ina kira da ‘yan kwangilar dake aikin da su kammala aikin da wuri cikin lokacin da a ka dibawa aikin”. Ganduje

Da yake jawabi a madadin a’lummar karamar hukumar Rano, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ya godewa gwamnatin Kano bisa wannan tagomashi da ta yi a garin na Rano.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci gidan asalin masarautar Rano jim kadan bayan gudanar da sallar juma’a, inda kuma mika mukullin gidan da gwamnati ta baiwa iyalan tsohon sarkin Rano.

Continue Reading

Ilimi

Daliban JSS3 za su koma makaranta nan da kwana biyu

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da ranar Lahadi 16 da kuma Litinin 17 ga watan Agusta a matsayin ranakun dawowa makarantar daliban sakandire aji na uku a jihar wato JSS3.

Matakin ya biyo bayan amincewa da gwamnatin ta yin a baiwa daliban damar tunkarar jarabawar su ta matakin aji na uku wanda daga ita za su tafi ajin gaba na manya wato SS1.

Cikin wata sanarwa da babban Sakataren ma’aikatar ilimi ya fitar a jihar, Phoebe Sukai Yayi, ta ce a na sa ran daliban JSS3 za su yi jarabawar karshe ta fita zuwa ajin gaba na SS1 a ranar 24 ga watan Agustan da mu ke ciki, domin haka ma’aikatar ilimi ta umarci dukannin shugabannin makarantun jihar da su tsara yadda za su karbi daliban makarantun kwana a ranar 16 da kuma daliban jeka ka dawo a ranar 16 ga wannan watan na Agusta.

Sanarwar ta kuma umarci dukannin makarantun gwamnati da na masu zaman kan su da su bi matakan kariya na Covid-19 a dukannin makarantun su domin kare daliban daga kamuwa daga cutar.

Ma’aiakatar ta kuma ce nan gaba za ta sanar da ranakun da sauran daliban ajin SS1 da SS2 da JSS1 da JSS2 tare da kuma daliban Primary.

Sai dai kuma ma’aiakatar ta ce za ta ci gaba da bin matakin koyar da dalibai daga gida ta hanyar kafar internet da gidan Talabijin da rediyo kafin a dawo karatu ka’in da na’in.

Continue Reading

Labarai

NUJ: Ku rinka yin taka tsan-tsan ‘yan jarida – Kwamrade Abbas

Published

on

Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta jihar Kano, Kwamared Abbas Ibrahim, ya bukaci ‘yan jarida musammam ma su dauko labarai daga kotuna da wuraren ‘yan sanda da su rinka yin taka tsan-tsan dan gudun kada su ma su yi laifi a kan aikin su.

Kwamared Abbas Ibrahim ya bukaci hakan ne jim kadan bayan kammala gabatar da wata mukala a wajen wani taron karawa juna sa ni da ‘yan jarida ma su dauko labarai daga kotuna da wuraren ‘yan sanda a jihar Kano.

Ya ce”Ma su dauko labaran kotu su guji kiran wadan da a ke tuhuma da ma su laifi har sai an yanke hukunci”.

A nasa jawabin shugaban ma su dauko labari daga kotuna a jihar Kano, Kwamared Muhammad Kabir Ya’u, cewa ya yi”Mun hada bitar ne, domin karawa juna sa ni, da karin kwarewa da wajen dauko labari daga kotu”.

wasu daga cikin wadan da su ka halarci bitar sun nu na jin dadi da farin cikin su, da kuma yadda bitar za ta kara mu su gogewa wajan gudanar da ayyukan su.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, Barista Maryam na daya daga cikin wadan da su ka gabatar da makala a wajen, ta shawarci ‘yan jarida idan sun fara daukar labari su rinka kai har karshen sa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish