Connect with us

Wasanni

Rugby: Za a dawo gasar a watan Oktoba

Published

on

Hukumar kwallon wasan Rugby ta amince a dawo gasar cin kwallon Rugby na duniya bangaren mata da maza a watan Oktoba.

Za a dawo gasar a ranar 24 da kuma 31 ga watan Oktoba, duk da cewa za a huta ranar 7 da kuma 8 ga watan Nuwamba kafin a ci gaba da gasar.

Kasashen da su ke fafatawa a gasar sun hadar da: kasar Afrika ta Kudu da New Zealand da Australia da kuma Argentina.

Wasanni

UEFA: Ta ci tarar PSG da gargadi mai karfi ga kocin ta

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kasar Faransa sakamakon kin fara wasa da ta yi da wuri bayan ta dawo daga hutun rabin lokaci.

Paris Saint-Germain ta samu nasara zuwa wasan kusa da na karshe a hannun Atalanta ta kasar Italiya da ci 2-1.

PSG za ta biya Yuro dubu 30, sannan kuma hukumar ta gargadi mai horas da PSG, Thomas Tuchel bisa bijre dokokin hukumar da ya yi.

A yau juma’a ne hukumar ta UEFA, ta fitar da sanarwar a kan matsayar da ta cimma sakamakon zama da ta yi a kan kungiyar PSG.

Wasan da a ka fafata a ranar Laraba a birnin Lisbon, wanda kungiyar Atalanta ta fara samun nasara da ci 1-0 da nema bayan da a ka dawo hutun rabin lokaci PSG ta farke sannan ta kara kwallo ta biyu a minti 9o.

Continue Reading

Wasanni

Gwarzon dan wasa: Arnold ya lashe kyautar bayan ya doke ‘yan wasan Man United 3

Published

on

Dan wasan gefefn bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Trent Alexander-Arnold ya zama gwarzon dan wasa ajin matasa na kasar Ingila bayan da ya doke ‘yan wasan Manchester United.

Arnodl, mai shekaru 21 dan kasar Ingila ya samu nasara ne bayan da magoya baya su ka zabe shi a matsayin gwarzon dan wasan gasar Firimiya na wannan kakar.

Dan wasan ya samu nasarar zura kwallayen da su ka tallafa Liverpool ta lashe gasar Firmiyar kasar Ingila a bana wanda ya kawo karshen shekaru 30 da kungiyar sa ta yi ba ta dauki gasar ba.

Kwallaye 12 da dan wasan Alexander-Arnold, ya zura su ne su ka ciciba kungiyar sa wajen bas hi damar lashe kyautar inda ya doke ‘yan wasan Manchester United ciki akwai, Mason Greenwood da Anthony Martial da kuma Marcus Rashford.

Cikin zaben su ma sauran ‘yan wasa ciki akwai na Chelsea Christian Pulisic da kuma Mason Mount tare da dan wasan Aston Villa, Jack Grealish da kuma na Sheffield United, Dean Henderson.

Kyautar dai ‘yan wasa ma su hazaka wadanda shekaru ya kai kasa da 23 wanda magoya bayan gasar Firimiya ke fitar da gwani a cikin su a duk shekara.

Alexander-Arnold ko a shekarar bara dan wasan sai da ya lashe kyautar bayan da ya takwarorin sa Jordan Henderson da Sadio Mane da kuma Kevin De Bruyne da Jamie Vardy tare da Nick Pope da Danny Ings.

 

Continue Reading

Wasanni

Mace ta maye gurbin na miji a matsayin kocin Ingila

Published

on

Mai horas da kasar Holland a bangaren mata, Sarina Wiegman za ta karbi kocin kasar Ingila a bangaren mata a kwallon kafa, Phil Neville.

Sarina tsohuwar ‘yar wasa mai taka leda a tsakiya a kasar Holland, ta rattaba hannu na tsawon shekaru 4 a kasar Ingila wanda a yanzu haka ta ke jiran Neville ya bata waje a kaka mai kamawa.

Sarina Wiegman mai shekaru 50, ta kai kasar Holland zuwa gasar Olympic da aka yi niyar yi a Tokyo na shekarar 2021.

Daraktan wasanni a hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila a bangaren mata, Baroness Campbell ta ce”Sarina ita ce zamun mu ta farko”.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish