Connect with us

Ilimi

BUK: Bin Allah zai sa a samu nasara a rayuwa – Farfesa Auwal

Published

on

A hudabar sa ta idin babbar Sallah, limamin masallacin Sabuwar Jami’ar Bayero a jihar Kano, Farfesa Auwal Abubakar ya gargadi al’ummar musulmi da su dage wajen taimakon al’umma tare da kabbara ga Allah, domin samun kusanci ga Allah ubangiji.

Farfesa Auwal Abubakar ya bayyana hakan ne jimkadan bayan Idar da sallar Idin babbar Sallah.

Y ace”Al’ummar musulmi su kasance sun bi Allah, sannan za su samu nasara a dukkan lamauran su na rayuwa”.

A nasa jawabin shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil cewa ya yi”Al’umma su zama ma su bin ka’ida da Jami’an lafiya su ka shimfida na kariya daga annobar Covid 19”.

Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya rawaito cewa an gabatar da sallar da misalin karfe 8:30 na safe tare da bin dokar sanya makarin hanci da baki.

Ilimi

Daliban JSS3 za su koma makaranta nan da kwana biyu

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da ranar Lahadi 16 da kuma Litinin 17 ga watan Agusta a matsayin ranakun dawowa makarantar daliban sakandire aji na uku a jihar wato JSS3.

Matakin ya biyo bayan amincewa da gwamnatin ta yin a baiwa daliban damar tunkarar jarabawar su ta matakin aji na uku wanda daga ita za su tafi ajin gaba na manya wato SS1.

Cikin wata sanarwa da babban Sakataren ma’aikatar ilimi ya fitar a jihar, Phoebe Sukai Yayi, ta ce a na sa ran daliban JSS3 za su yi jarabawar karshe ta fita zuwa ajin gaba na SS1 a ranar 24 ga watan Agustan da mu ke ciki, domin haka ma’aikatar ilimi ta umarci dukannin shugabannin makarantun jihar da su tsara yadda za su karbi daliban makarantun kwana a ranar 16 da kuma daliban jeka ka dawo a ranar 16 ga wannan watan na Agusta.

Sanarwar ta kuma umarci dukannin makarantun gwamnati da na masu zaman kan su da su bi matakan kariya na Covid-19 a dukannin makarantun su domin kare daliban daga kamuwa daga cutar.

Ma’aiakatar ta kuma ce nan gaba za ta sanar da ranakun da sauran daliban ajin SS1 da SS2 da JSS1 da JSS2 tare da kuma daliban Primary.

Sai dai kuma ma’aiakatar ta ce za ta ci gaba da bin matakin koyar da dalibai daga gida ta hanyar kafar internet da gidan Talabijin da rediyo kafin a dawo karatu ka’in da na’in.

Continue Reading

Ilimi

Zamfara: Yara miliyan daya ne basa zuwa makaranta – Abubakar Maradun

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce kimanin yara miliyan daya ne ba sa zuwa makaranta a fadin jihar.

shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun ne bayyana hakan yayin zantawa da manema.

Ya ce,“Sakamakon wancan matsalar, tuni gwamnatin jihar ta bullo da wani shiri na inganta karatun boko da na allo, da kuma ciyar da almajirai a makarantun allon su”.

Ya kuma ce,“Shirin ya samo asali ne daga wata kidaya da a ka yi, da ta nuna cewa a Najeriya akwai yara miliyan goma da ba sa zuwa makaranta, kuma miliyan daya daga cikin su ‘yan jihar Zamfarawa ne”. A cewar Alhaji Abubakar Aliyu

Alhaji Abubakar Aliyu Maradun, ya kara da cewa, babbar manufar ita ce bai wa wadannan yara damar samun ilimin a dukkanin bangarorin biyu, da kuma dakile matsalar barace-barace a fadin jihar.

 

Continue Reading

Ilimi

Za a ci gaba da shari’a a kan makarantar magada

Published

on

Babbar kotun shari’ar muslinci mai zamanta a filin Hockey dake unguwar Hausawa a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Aliyu Muhammad Kani, ta sanya ranar 28 ga wannan watan domin ci gaba da shari’ar takaddama tsakanin magadan marigayi Muhammad Bello Buba, a kan batun wata makaranta wadda a ka ce marigayin ya barta a matsayin hubusi.

A zaman kotun na ranar Juma’a an yi umarnin a je a raba kayan gadon, wadanda babu takaddama a kan su.

A nayin takaddamar ne dai a kan wata makaranta mai suna, Rauda Fitta Alimul’umma , wadda take unguwar Bompai .

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail da ya halarci zaman kotun ya so zantawa da wasu daga cikin magadan sai dai sun ki cewa komai.

Muhammad Albakari mika’il kwamishana na biyu a hukumar Zakka da Hubusi ya bayyana cewar alhakin su ne su kare duk wani abu da a ka barwa al’umma a matsayin hubusi.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish