Connect with us

Ilimi

MKG: Ta shuka bishiyoyi domin dakile kwararowar Hamada a Kano

Published

on

Gamayyar matasan Kano da ke gangamin dasa bishiyoyi a jihar Kano (Make Kano Green) ta dasa Bishiyoyi 1,567 a kananan hukumomi biyar a jihar.

Babban jami’I a kungiyar, Isma’il Auwal ne ya bayyana hakan, a ganawar sa da Dala FM ranar Lahadi, lokacin da su ke ci gaba da shuka Bishiyoyi a yankin Yalwa dake unguwar Mariri a karamar hukumar Kumbotso.

A cewar sa” Mun samu hadin kan al’umma, wajen gudanar da gangamin dashen Bishiyoyin, haka kuma mu na bibiyar dukkanin wuraren da mu ka dasa shuka, domin ganin halin da suke ciki a lokaci da kuma bayan lokaci”.

A nasa bangaren mai unguwar Yalwa, Alhaji Abdullahi Shehu ya ce,” Mun yi farin ciki da wannan gangami, sannan na yi alkawarin yin shiri na musamman, domin kula da bishiyoyin da a ka dasa wajen ganin ba su lalace ba”.

Sai dai irin wannan yunkuri da matasan ke yi, na fuskantar barazana, musamman daga masu dabi’ar saran itace, wadanda mafi yawa na kallon yunkurin yaki da kwararowar hamada matsayin kamar wasa ne zancen.

Haka kuma mafi yawan ‘yan Nijeriya na sare Bishiyoyi, duk da dimbin iskar Gas da kasar ke da ita.

Kwamaret Sani Musa Idris, wani dan gwagwarmaya ne mai fafutukar kare muhalli a Kano, ya ce”Akwai bukatar kara zage damtse wajen yin dashen Bishiyoyin, domin magance matsalar kwararowar hamada”.

Wakilin mu Bashir Sani Abubakar ya rawaito cewa ko a shekarar 2010, hukumar raya al’adun Birtaniya da hadin gwiwar hukumar raya gandun daji ta jihar Kano, sun gabatar da wani shirin yin dashe a jihar, domin magance kwararowar Hamada, wanda su ka dasa bishiyoyi dubu takwas a wancan lokaci.

Ilimi

SUBEB: Za mu gina sababbin ajujuwa da gyara wasu makarantun Kano

Published

on

Gwamantin jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan Uku, domin gina sabbin ajujuwa da kuma gyare-gyaren makarantu a fadin jihar Kano.

Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB), Dr. Danlami Hayyo ne ya tabbatar da hakan yayin zantawar su da wakiliyar mu Zahrau Nasir.

Ya ce, “Ayyukan da za a yi sun hadar da haka rijiyoyin burtsatse a makarantu da sayen kujerun da yara za su rinka amfani da su a makarantu da sauran su”.

Ya kuma ce, “Tuni wadannan kudade su ka shiga asusun hukumar ta SUBEB wanda da zarar gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dawo za a kaddamar da fara aikin”. A cewar Dr. Danlami Hayyo.

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, Dr. Danlami Hayyo ya kuma ce, baya ga ware wadannan kudaden gyaran makarantun, akwai kuma Babura da gwamnatin ta saya, domin rabawa masu duba makarantu a kananan hukumomi wajen amfani da su a wuraren da motoci ba sa iya shiga.

 

Continue Reading

Ilimi

Kada gwamnoni su bude makarantu sai an ba su umarni – Boss Mustapha

Published

on

Gwamantin tarayya ta ce, lokacin buɗe makarantu bai yi ba, kuma tana gargaɗin gwamnonin jihohi da kada su karya dokar da ta bayar ta buɗe makarantu ba tare da sahalewar ta ba.

Shugaban kwamitin karta-kwana na fadar shugaban ƙasa da ke yaƙi da cutar Corona kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapaha ne ya bayyana hakan, a wani taro da ya gudana kan hanyoyin kaucewa cutar corona.

Ya ce, “Ba daidai ba ne gwamnatocin jihohi su bude makarantu ba tare sahalewar ta ba, sannan su ƙara shiri kan yadda za su kare dalibai tare da malaman su”. Inji Boss Mustapaha

 

Continue Reading

Ilimi

Idan a ka bude jami’o’i ba’a cika mana alkawaru ba za mu tafi yajin aiki – SSANU

Published

on

Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’i ta kasa SSANU ta ce, idan har gwamnatin tarayya ta bude makarantun kasar nan ba tare da cika ma ta alkawuranta ba, shakka babu za ta tsunduma yajin aiki.

Mataimakin shugaban kungiyar Alfred Jimoh ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema Labarai a Jami’ar Ibadan.

Ya ce, “Idan har gwamnatin za ta duba yiwuwar bude makarantu to kamata ya yi ta kara nazartan biya mana bukatun mu, da nufin bai wa dalibai manyan makarantu komawa makaranta”.

Alfred Jimoh ya kuma ce, “Daga cikin bukatun ‘ya’yan kungiyar akwai biyan su alawus-alawus wanda gwamnatin ba ta biya mu ba tun daga shekara ta dubu biyu da tara zuwa yanzu”.  Inji Alfred Jimoh

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!