Connect with us

Labarai

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta koka kan matsalar tsaro

Published

on

Kungiyar gwamnoni a Najeriya ta koka kan kalubalen da ke cigaba da dabaibaye bangaren tsaro a fadin kasar.

Shugaban kungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi a wata sanarwa da ya fitar ta nuna damuwa kan abin da ya faru ga gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Sanarwar ta koka kan abin da ya faru da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, tare da tawagarsa, wanda mayakan Boko Haram suka kaiwa hari a makon jiya.

Sanarwar ta ce, “A madadin gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Najeriya a karkashin kungiyar NGF, muna bayyana goyon bayan mu ga gwamnan Zulum da al’ummar jihar Borno, biyo bayan harin ranar Laraba da ta gabata, wanda wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kaddamar. Wannan wani hari ne na bazata. Hakan kuma ya nuna karara cewa akwai rauni sosai a tsarin tsaron kasar mu. Duk da cewa ka tsallake rijiya da baya, sai dai abun a koka ne bisa raunikan da wasu daga cikin tawagar suka samu”.

“Mai girma gwamna, membobin wannan kungiya a shirye suke su mara maka baya wajen dakile matsalolin da suka dabaibaye bangaren tsaro, domin kawar da ayyukan masu tayar da kayar baya a jihar Borno. Mun damu matuka da halin rashin tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar nan, duk kuwa da kokarin da gwamnati ke yi na kawo karshen sa. Domin haka zamu gudanar da tattaunawa ta musamman da kuma shawarwarin da ya kamata mu tunkari shugaban kasa da su, da kuma hafsoshin tsaro”.

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Trending