Connect with us

Wasanni

Horaswa: Ljunberg ya bar Arsenal

Published

on

Mataimakin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Freddie Ljunberg ya ajiye aikin sa a matsayin mataimakin mai horas da kungiyar.

Ljungberg mai shekaru 43 ya dai kama aiki a matsayin mai horaswa na rikon kwarya a Arsenal, tun bayan korar Unai Emery da kungiyar ta yi a watan Nuwambar shekar 2019.

Ljunberg tsohon dan wasan kungiyar kuma tsohon dan wasan kasar Sweden, ya na daya daga cikin ‘yan wasan da Arsene Wenger ke ji da shi a shekarar 2003-04, sai dai kuma ya koma mataimakin mai horaswa a karkashin Mikel Arteta.

Haka kuma Ljungberg, ya jagoranci kungiyar Arsenal ‘yan kasa da shekaru 15 da 23 a matsayin mai horaswa a baya.

Ya ce“Na yanke shawarar barin kungiyar a matsayin mataimaki, ina so ni ma ma samu ci gaba, domin na zama ina horas da kungiya, kuma tun shekarar 1998 na ke kungiyar Arsenal, na samu dama da yawa har na zama koci tun daga matakin dan wasa, saboda haka ina yi wa Arteta da kuma sauran ‘yan wasa fatan samun nasara a wannan kakar da za a fara, ina fatan za mu kara haduwa da su a nan gaba” Ljunberg.

Tuni daraktan wasannin kungiyar, Edu ya bayyana cewar”Tabbas mun ji haushin tafiyar Freddie, domin kuwa mun san yadda ya ke son Arsenal”.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending