Connect with us

Wasanni

Champions League: Tarihin da a ka kafa a bana

Published

on

Kungiya kwallon kafa ta Bayern Munich ta ci kwallaye 500 a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai, bayan da dan wasan gefen ta Kingsley Coman ya tallafawa kungiyar a daren jiya Lahadi ta lashe gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai karo na 6 a hannun PSG.

Real Madrid it ace ja gaba a duniya da kwallaye 567 a raga cikin gasar sai Barcelona da kwallaye 517.

Nasarar da Bayern Munich ta samu yanzu haka ta kama kungiyar Liverpool, sai dai Real Madrid ce mai kofi 13 AC Milan da kofi 7.

Wannan ne karo na farko da kungiyar Paris Saint-Germain ta kasa samun nasarar wasa a cikin wasanni 35 da ta yi, tun lokacin da Manchester City ta doke ta da ci 1-0 a watan Afirilu na shekarar 2016.

Bayern ta zama kungiya ta farko a nahiyar turai da ta samu nasarar lashe gasar a dukannin wasanni 11 da ta yi ba tare da an doke ta ba.

Wannan ne karo na hudu da dan shekaru 55 da kwanaki 181 wato Hansi Flick mai horaswa ya lashe gasar, tun bayan Raymond Goethals lokacin da ya ke horas da Marseille a shekarar 1993 wanda ya lashe gasar ya na da shekaru 71, sai Jupp Heynckes mai shekaru 68 wanda ya lashe gasar da Bayern Munich a shekarar 2013 da kuma Alex Ferguson mai shekaru 57 wanda ya lashe gasar da Manchester United a shekarar 1999 da kuma 2008 lokacin ya na da shekaru 66.

Dan wasan gaban kungiyar Bayern Munich, Coman ya zama dan kasar Faransa na biyar da ya buga wasan karshe a gasar da ya zura kwallo ya lashe gasar, sai Karim Benzema a shekarar 2018 da Zinedine Zidane a shekarar 2002 da Marcel Desailly a shekarar 1994 da kuma Basile Boli a shekarar 1993.

Mai tsaron ragar PSG, Keylor Navas, ya zama mai tsaron raga na uku da ya buga wasan karshe a gasar da kungiya biyu Real Madrid da PSG, tun bayan Jorg Butt wanda ya buga a Munci da Bayer Leverkusen sai kuma Edwin van der Sar Manchester United da Ajax.

Dan wasan bayan PSG, Thiago Silva ya zama dan wasan kasar Brazil na farko da ya fara zuwa wasan karshe a gasar nahiyar turai na Europa da kuma wasan karshe na Champions League a matsayin Kyaftin.

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending