Connect with us

Labarai

Iyayen da su ka daure dan su tsawon shekaru 7 sun gurfana a kotu

Published

on

Kotun majistret mai lamba 18 da ke titin Zingeru, karkashin mai shari’a Muhammad Idris ta fara sauraron wata Shari’a wadda ‘yan sanda su ka gurfanar da wasu mutane 2 miji da mata wadanda a ke zargin su da lefin hada baki da tauye hakkin dan adam.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar, wanda a ke zargi na farko Malam Ibrahim Aliyu ya hada baki da matar sa Fatima Lawan sun kulle Dan sa na cikin sa a daki tsahon shekaru 7.

Kunshin zargin ya kuma bayyana cewar, wasu makotan Malam Lawan su ne su ka kaiwa ‘yan sanda labari cewar, ya kulle  dan sa a daki dan ya na da tabin hankali.

Yayin da a ka karanta mu su tuhumar sun musanta zarge-zargen, inda lauyan su Barister Hassan Sani Adamu ya roki kotun da ta sanya su a hannun beli kasancewar wanda a ke tuhuma na farko dattijo ne mai kimanin shekaru 60 wadda a ke tuhuma ta biyu tana da kananun yara guda 6 kuma suna mukatar kulawar su hadda ma wadda a ke shayarwa katanan kuma a kotu

Sai dai mai gabatar da kara Badamasi Ya’u Gawuna ya yi kakkausar su ka ga rokon inda ya bayyanawa kotun cewar, ba su kammala bincike ba kuma su na tsoron kada a bayar da belin wanda a ke tuhuma su tsere ko kuma su yiwa binciken ‘yansanda katsalandan, kuma yanzu haka Ibrahim ya na asibiti cikin mawuyacin hali.

Yayin da yake kwarya-kwaryar hukunci mai shari’a Muhammad Idris ya bayyana cewar, laifin da a ke tuhumar mutanan laifi ne da za a iya bayar da beli.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, Mai shari’a ya bayar da belin su a kan sharadin sai sun gabatar da mai gari ko mai unguwa sannan sai sun kawo wani mutum daya mai kima da mutunci za kuma aje a ga gidajen masu karbar belin idan kuma suka tsere wadanda suka karbe su za su biya Naira duba dari, kuma kotun ta sanya ranar 2 ga watan gobe dan a sake gabatar da su.

Domin jin tattaunawa da wadanda a ke zargi saurari wannan.

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Labarai

Abin takaici ne yadda ake fuskantar ƙarancin ruwan Sha a sassan jahar mu – Gwamnan Kano.

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nuna rashin jin daɗin sa bisa yadda ake samun ƙarancin Ruwan Sha, a wasu daga cikin sassa jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, a lokacin a ya kai ziyarar gani da ido, matatar Ruwa da ke Tamburawa a yammacin yau Juma’a, a ƙokarin sa na na gyara ɓangaren ruwan a cikin garin Kano.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma sha alwashin tabbatar wa al’umma cewar, gwamnatin sa za ta yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da isasshen ruwan Sha ga al’ummar jihar Kano.

Gwamnan ya ƙara da ce a lokacin da suka zo ba sufi mako biyu ba suka samar da ingantaccen Ruwan sha, wanda ya rinƙa shiga cikin lunguna da Sako na sassan jihar.

Continue Reading

Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da sayar da Burtalai a wasu garuruwan ta

Published

on

Biyo bayan kokawar da wasu Fulani Makiyaya suka yi kan yadda wasu suka gididdiba burtalai yayin da aka siyarwa Manoma, a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, yanzu haka ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da taɓawa, ko kuma sayar da dukkanin Burtalan kiwon shanun ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban riƙon ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu a kan taɓa dukkan guraren, a dan haka sun dakatar da dukkanin yunƙurin taɓa Burtalan har sai shugabanni na kwamitin ƙasa sun kammala bincike wanda yanzu haka ake ci gaba da yi.

Da yake nuna jin daɗin sa kan matakin dakatarwar, amadadin Fulanin garuruwan, shugaban ƙingiyar Funali Makiyaya ta Gan Allah, Ahmad Shehu Gajida, yabawa gwamnatin jihar Kano, da kuma ƙaramar hukumar ta Tofa ya yi, bisa karɓar koken su da suka akai.

A baya-bayan nan ne dai a zantawar Dala FM Kano, da wasu Funalani Makiyaya mazauna garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, suka koka kan yadda aka gididdiba burtalan a yankunan nasu aka siyarwa manema, lamarin da suka ce ka iya sawa su rasa guraren da za suyi kiwon shanun su wanda hakan babbar barazana ce a gare su.

Continue Reading

Trending