Connect with us

Wasanni

Greece: Kotu ta yankewa Harry Maguire hukunci

Published

on

Mai horas da kasar Ingila, Gareth Southgate, ya cire dan wasan bayan kasar Harry Maguire daga jerin cikin ‘yan wasan Ingila da za su buga wasan cancanta na shiga gasar cin kofin kasa da kasa na nahiyar Turai.

Mai horaswar ya tsige sunan Maguire, 27 kuma dan wasan bayan Manchester United, daga cikin ‘yan wasan sa sakamakon samun sa da laifi da Kotu ta yi a garin Syros dake tsibirin Mykonos a kasar Girka.

A jiya Talata ne dai kotu ta tabbatar da dan wasan da samun sa da laifin, fadar kalamai marasa dadi ga jami’an ‘yan sanda da bijirew yayin da a ka yi kokarin kama shi da kuma laifin bayar da cin hanci.

Southgate ya ce “Na cire sunan dan wasan ne saboda, ya na gaban kotu a yanzu”.

Kotun dai ta daure Maguire har tsawon watanni 21 da kwanaki 10 a gidan Kurkuku tare da dakatar da shi daga shiga yankin na Mykonos har na tsawon shekaru uku, bisa samun dan wasan da laifi dumu-dumu.

Sai dai dan wasan ya ce“Tuni na daukaka kara ta hannun Lauyoyi na nan take, kuma ina da kwarin gwiwa, saboda ba ni da laifi, domin kuwa wannan ya shafi iyalai na, abokai na da kuma ni kai na”. inji Maguire.

Tun makon da ya gabata ne dai ‘yan sanda a kasar Girka su ka tsare Maguire na tsawon kwanaki biyu a lokacin da ya ke wani wajen shakatawa a kasar.

Kasar Ingila za ta fafata ne da kasar Denmark da kuma Iceland a wata mai kamawa a wasan cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa.

 

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending