Connect with us

Wasanni

Shari’ar Maguire: An ragewa dan wasan wa’adain da zai yi a gidan Kurkuku

Published

on

Kotu a kasar Girka ta rage hukuncin da ta yi wad an wasan bayan Manchester United Harry Maguire, daga watanni 21 da kwanaki 10 a gidan Kurkuku zuwa watanni 13.

Kotun ta janye hukuncin da ta yankewa dan wasan daga shekaru 3 a baya shi da dan uwan sa tare da wani abokin sa.

Maguire mai shkearu 27, da dan uwan sa Joe Maguire mai shekaru 28 da kuma Christopher Sharman mai shekaru 29 an same su da laifi.

Mahaifin Maguire Alan, shi ne dai ya halarci zaman kotun a jiya Talata tare da Anagnostakis daya daga cikin lauyan sa kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam wanda ya roki kotu da ta dakatar da dokar da ta yanke, sai dai kuma tuni alkalan kotun su ka yi watsi da bukatun sa.

Dukannin su ukun da a ke zargi sun karya ta zargin da a ke yi mu su a baya. Sai dai daya daga cikin ‘yan sanda da lamarin ya faru a gaban sa ya shaidawa kotun cewa dan wasan ya fada mu su cewa “Ko kun san ni waye? To ni ne Kyaftin din Manchester United, kuma ni mai kudi ne, kuma zan baku, zan biya ku, ku bari mu tafi”. A cewar sa.

Su kuwa abokan sa sun ce Maguire ya fadi cewa”Ku bari mu tafi, ni mai kudi ne kuma zan biya, ni ne jagoran kungiyar Manchester United.

Sai dai Lauyan mai kare Maguire ya ce an samu sabani na harshe ne a tsakanin juna, domin kuwa Maguire ya na nufin nawa ne tarar da a ka yi masa zai biya a sake su.

Lauyan Maguire, Anagnostakis ya ce“Kwararru masu bincike sun tabbatar an lakada musu duka a lokacin, shi ya sa ma Maguire ya ji haushi ya kai duka da kafar sa”.

Shi kuwa Dr Ioannis Paradissis, wanda ya wakilci ‘yan sanda biyu wanda lamarin ya faru a gaban su, ya ce“Na yi matukar mamaki kuma kamar ba wani dan was aba, domin kuwa Maguire ko hakuri bai bayar ba a lokacin”.

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending