Connect with us

Labarai

Kotu na tuhumar matashi da bata sunan budurwa a Facebook

Published

on

Kotun majistret mai lamba 86 karkashin mai shari’a Faruk Ibrahim Umar ta sanya wani matshi a hannun beli.

Matashin mai suna Abubakar Muhammad a na zargin shi da laifin bata suna ta hanyar sanya hoton wata budurwa Aisha Ibrahim Babaji, ya hada ta da hotunan batsa ya na yadawa a dandalin sada zumunta na Facebook.

Yayin da a ka karanta tuhumar ya musanta zargin lauyan sa ya roki kotun da ta bayar da belin sa.

Mai shari’a Faruk Ibrahim Umar ya amince da rokon, sai dai ya ayyana cewar, sai an gabatar da mutum 2 masu kima kuma wadanda su ke da gida a karkashin hurumin kotun idan kuma ya tsere za su biya miliyan daya kowannen su.

A zantawar wakilin mu da lauyan mai kara Barista Husaini Ahmad Makari ya ce, “A na zargin Abubakar Muhammad ne da yada hoton batanci ga Aisha Babaji yayin da ya ke yanke fuskar ta yada hotunan tsiraici har ma da kawayen ta da su ka saka baki, bayan bincike a ka gano shi kuma a ka gurfanar da shi a gaban kotu”.

Itama Aishar ta bayyana yanda ta ji lokacin da hotunan ta suke yawo a Facebook tare da hotunan batsa.

Ta na mai cewa, “Mun hadu da shi ne a wajen aiki sai ya nuna ya na so na har ya ce zai turo nan bada dadewa ba, sai na ce ya yi hakuri sai nan gaba, shi ne ya dauki hotuna na ya na hadawa ya turawa kawaye na da ‘yan uwa na, ni yanzu ina so a bi min hakki na”. A cewar Aisha Babaji.

Lauyan da ya ke kare matashin, Barista Aliyu Umar Faruk ya bayyana matsayar su a kan batun inda ya ce, “Na farko dai tuhuma ce kamar yadda ‘yan sanda su ka saba yi, amma har yanzu a idon shari’a shi ba mai laifi ba ne, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya nuna, saboda haka kotu ce kawai za ta iya tabbatar da mai laifi ne ko ba mai laifi ba ne”.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Kotun ta sanya ranar 8 da 9 ga wata domin fara sauraron shaidu.

 

 

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending