Connect with us

Labarai

Ganduje zai gina wa kungiyar masu fama da lalurar laka cibiya

Published

on

Kungiyar masu fama da lalurar laka ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gina mu su cibiyar da za su rinka gudanar da al’amuran su.

Shugaban kungiyar Injiniya Abdul Danladi Haruna ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin jihar Kano.

A ranar Asabar 04 ga watan Satumba ne a ke gudanar da bikin ranar masu fama da lalurar laka ta duniya.

Ya ce, “Samar mana da cibiyar zai taimaka gaya wajen rika gudanar da al’amuran mu da dama duba da kalubale da masu lalurar ke fuskanta”.

Da yake jawabi Mai Martaba sarkin Kano Wanda Alhaji Habib Bello Dankadai ya wakilta ya bukaci masu hannu da shuni tare da gwamnati wajen rika taimakawa masu lalurar ta laka.

Da yake jawabi yayin taron gwamna Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda mataimakin sa Nasir Yusif Gawuna ya wakilta ya ce, “Kofar mu a bude take wajen taimakon masu fama da wannan lalura, duba da koken da suka yi na bukatar a biya musu kudin haya na ofishin su, gwamnati za ta biya musu na shekara biyu, kuma kafin wa’adin kudin ya kare gwamnatin za ta gina musu cibiyar da su ke bukata”. A cewar Nasir Yusuf Gawuna

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, a yayin taron mataimakin Gwamnan Kano ya kuma mika kayan aikin ofishin da su ka rubuto wa gwamnatin su na bukata domin gudanar da ayyukansu.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending